Latest
Gwamnatin Kano ta fara shirin samar da sababbin birane da mutane za su koma su cigaba da rayuwa a wajen jihar. Abba Kabir Yusuf ya ce aikin zai rage cunkoso a Kano.
Wasu iyalai da suka haɗa da uwa da ƴaƴa uku sun riga mu gidan gaskiya bayan cin shinkafa a Ilorin, babban birnin jihar Kwara ranar Asabar da ta gabata.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya caccaki gwamnatin Bola Ahmed Tinubu bisa dawo da sabon samfurin biyan tallafin man fetur a Najeriya.
Hukumar ƴan sandan Najeriya ta gayyaci shugaban ƙungiyar kwadago ta ƙasa, Joe Ajaero kan zarge-zarge da suka haɗa da ɗaukar nauyin ta'addanci da sauransu.
Miyagu sun hana mazauna kananan hukumomi biyu; Musawa da Kankia a jihar Katsina sakat, yayin da su ka kai hari tare da sace mata da yara da magidanta.
Gwamnatin Kaduna ta fara daukar matakan rage illar da ambaliya ruwa za ta haifar a wasu daga cikin sassan jihar, inda gwamnati ta nemi kowa ya bar yankunan.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tsige shugaban hukumar alhazai ta ƙasa NAHCON kan badakalar aikin hajjin bana, ya naɗa Sheikh Farfesa Abdullahi Pakistan.
Kimanin magoya bayan jam'iyyar APC daga mazabar Ondo ta tsakiya a jihar Ondo ne suka sauya sheka zuwa PDP. Dakta Adeniran Oyebade ne ya jagoranci tawagar.
Tun bayan zaman majalisar magabatan kasa abubuwa da dama sun faru a Najeriya ciki har da sayen sabon jirgin Tinubu, maganar dawo da tallafin mai da kwace jirage.
Masu zafi
Samu kari