Latest
Rahotanni sun bayyana cewa Maria Branyas, wadda ta fi kowa a duniya ta mutu tana da shekaru 117. An ruwaito cewa an haifi Maria a 1907 kuma ta mutu a Spain.
Gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin mutum 10 wanda zai sa ido tare da tabbatar da an bi umarnin kotun ƙoli na ba kananan hukumomi ƴancin cin ganshin kai.
Al'ummar mazabar Ondo ta Gabas/Ondo ta Yamma sun fara shirin yiwa dan majalisar da ke wakiltarsu a majalisar wakilai kiranye. Sun ce ya koma kasar waje.
Matasa a Misau da ke jihar Bauchi sun kwaci mutane biyu da ake zargi da yin kisan kai ga dan acaba daga hannun yan sanda sun kashe su har lahira.
Tsohon shugaban kungiyar NEITI, Waziri Adio ya bukaci kamfanin NNPCL ya fito ya yi bayani da kyau kan batun maido tallafin mai fetur da cire shi ga yan Najeriya.
Kotun daukaka kara ta umurci tsohon gwamna, Yahaya Bello da ya mika kansa domin a gurfanar da shi a gaban kuliya. Kotun ta yi watsi da hukuncin wata kotun Kogi.
Kungiyar kwadago ta bayyana cewa shugabanta, Kwamred Joe Ajaero ba zai iya mutunta gayyatar da ta yi masa ba bisa wasu dalilai, amma ya sa ranar zuwa.aa
Jam'iyyar NNPP ta sanar da kudaden da masu sha'awar tsayawa takara a zaben kananan hukumomin jihar Kano za su biya. NNPP ta sanya N600,000 a kujerar Ciyaman.
Sheikh Abdulrahaman Azzamfari ya nuna damuwa kan halin rashin tsaron da al'umma suka tsinci kansu a jihar Zamfara sakamakon hare-haren ƴan fashin daji.
Masu zafi
Samu kari