Latest
Matasan Najeriya a kafar X sun yi rubdugu ga Reno Omokri kan kokarinsa na kare gwamnatin tarayya kan sayen sabon jirgi ga shugaban kasa Bola Tinubu.
Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya shaidawa ƴan majalisar wakilai cewa adadin waɗanda suka rasu sakamakon ambaliyar ruwa ya kai 28 zuwa ranar Talata.
Gwamnatin Kano ta bayyana matsayarta kan zargin da ake yi na cewa an ba kamfanin kanin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso kwangilar magani ba bisa ka'ida ba.
Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta Kano (PCACC), ta samu umarni domin rufe wani asusu da ke dauke da kudade a binciken da take kan badakalar kwangila.
Babban limamin cocin nan da aka saba jin muryarsa a harkokin siyasar ƙasar ɓan, Primate Ayodele ya nemi shugaban ƙasa Tinubu ya sauke ministan wasanni
Daliban da suka kifar da gwamnatin kasar Bangladesh a yayin zanga zanga sun bayyana halin da suke ciki a asibiti. Ma'aikatan lafiya ta bayyana yadda suke aiki.
Yan majalisar kasar nan sun bukaci rundunar yan sanda ta janye tuhumar ta'addanci da ta ke yiwa shugaban NLC, Joe Ajaero, tare da bayyana tsoron dawowar zanga-zanga.
Dakarun rundunar sojojin sama sun samu nasarar hallaka manyan kwamandojin 'yan ta'adda a jihar Borno. Sojojin sun kashe su ne a wasu hare-hare ta sama.
Tsohuwar ministar ilimin Najeriya, Dakta Oby Ezekwesili ta bukaci Bola Tinubu ya cefanar da kamfanin NNPCL ga yan kasuwa idan yana son kawo cigaba a fannin.
Masu zafi
Samu kari