Latest
Malamin Musulunci, Sheikh Bello Yabo ya shawarci al'umma da su tabbatar sun mallaki makamai masu kyau domin kare kansu daga cin zarafin yan bindiga a Najeriya.
Legit Hausa ta tattaro abubuwan da ya kamata ku sani game da mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun, wadda ta gaji Olukayode Ariwoola a matsayin babban jojin Najeriya.
Mutanen yankin ƙaramar hukumar Ringim a jihar Jigawa sun yi zanga-zanga a kofar shiga gidan gwamnatin jihar jiya Alhami, sun nemi a tsige kwamishina.
Gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta yi alkawarin karasa dukkan ayyukan da gwamnatocin baya kamar Muhammadu Buhari da Goodluck Jonathan suka bar mata.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya rantsar da Justice Kudirat Kekere-Ekun matsayin sabuwar shugabar alkalan Najeriya a yau Juma'a 23 ga watan Agustan 2024.
Gwamnatin tarayya ta shirya ganawa da kungiyar malaman jami'o'in Najeriya domin tattaunawa kan bukatunsu da nufin hana su shiga yajin aikin da suka kuduri aniya.
Babbar alkalin jihar Akwa Ibom, mai shari'a Ekaete Obot ta yi afuwa ga fursunoni 44 a gidan yari. An sake wanda ya sace tukunyar mahaifiyarsa bayan shekara daya.
Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya yi Allah wadai da kisan Sarkin Gobir hakimin Gatawa, Isah Bawa, ya ce ba zai yiwu makasan basaraken su ci bulus ba.
Mataimakin shugaban majalisa, Sanata Barau I Jibrin ya ce gwamnati ta na iya kokarin tallafawa talakawa, amma daidaikun mutane su na hana ruwa gudu.
Masu zafi
Samu kari