Latest
Rahotanni sun nuna cewa an canza ranar taron gwamnatin tarayya da ASUU daga ranar Litinin zuwa ranar Laraba, ana kokarin hana shiga yajin aiki a Najeriya.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin Adeola Ajayi a matsayin sabon Darakta-Janar na hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) bayan murabus din Yusuf Bichi.
Bayan rikicin yan Shi'a da yan sanda, an sake samun rikicin shugabanci a kasuwar Wuse da ke birnin tarayya Abuja inda mutane suka rufe shagunansu.
Wasu ‘yan ta'adda da ba a san ko su wanene ba ne sun kai wa kwamishinan muhalli na jihar Oyo, Honarabul Mogbanjubola Olawale Jagaban hari a ranar Litinin.
A ranar 26 ga watan Agusta ake murnar ranar Hausa a duniya. Legit Hausa ta tattaro muku hukuncin ranar Hausa a Musulunci, muhimmancin koyon ka'idojin rubutun Hausa
Rikicin shugabanci ta taso jam'iyyar APC a gaba a jihar Enugu. Tsagin da ke samun goyon bayan shugaban jam'iyyar na kasa, ya dakatar da mambobi 20.
Sabon rikici ya kunno a kai a APC reshen Benuwai yayin da tsagin kwamitin shugabancin rikon kwarya na Omale da na bangaren Austin Agada suka fara nunawa juna yatsa.
Za a ji cewa Babban Sufeton kasar nan, Kayode Egbetokun ya bayyana cewa sun yi nasarar kashe kasungurmin dan ta'adda a lokacin da su ka kai dauki ga dalibai.
Gwamnatin jihar Sokoto za ta gudanar da cikakken bincike kan wani zargi da UNICEF ta yi na cewa wasu ma'aikatan jihar sun karkatar da abincin jarirai.
Masu zafi
Samu kari