Latest
Wasu rahotanni sun sake bayyana kan dalilin murabus din hadimin Bola Tinubu, Ajuri Ngelale inda ake zargin ana neman dakatar da shi ko kuma sauya masa mukaminsa.
Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya fadi ainihin abin da ya haɗa shi faɗa da Adams Oshiomhole inda ya ce sun samu matsala ne saboda jana'izar Cif Tony Anenih.
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya amince da takardar ajiye aiki da hadiminsa, Ajuri Ngelale ya yi a jiya Asabar inda ya yi masa godiya da kuma fatan alheri.
An maido wani bidiyon Sheikh Kabir Gombe yana yabon gwamnatin APC a 2023. Jama’a sun yi ca a kan malamin addinin musuluncin lura da halin da aka shiga.
Ana tuhumar CBN da batar da biliyoyin kudi domin sayen motoci da sunan kama hayan gidajen haya. An yi sama da kusan N10bn domin motocin gwamna da mataimakansa.
Jam'iyyar APC reshen jihar Anambra ta sanar da cewa ba za ta shiga cikin zaben kananan hukumomin da za a gudanar a jihar ba. Ta dauki matakin zuwa kotu.
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya nuna alhini bayan rasuwar Hajiya Dada a jihar Katsina wacce ita ce mahaifiyar tsohon shugaban kasa, Umaru Musa Yar'Adua.
Kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya bayyana cewa babu tabbaci matatar Dangote za ta sanya farashin man fetur ya sauka a kasar nan. NNPCL ya yi karin gaske kan lamarin.
'Yan Najeriya sun bayyana mabanbantan ra'ayoyi kan murabus din da hadimin shugaban kasa Bola Tinubu ya yi. Ajuri Ngelale dai ya je hutu ne daga aikinsa.
Masu zafi
Samu kari