Latest
A wannan rahoton za ku ji cewa fitaccen malamin addinin musulunci Sheikh Bello Yabo ya yi martani ga kalaman yan bindiga na son sace shi. Ya ce ba a biyan fansa.
Sheikh Bello Yabo ya ce ko zai yi gaba da gaba da yan bindiga ba zai daina musu nasiha ba. Bello Yabo ya ce bai yarda yan bindiga za su iya galaba a kansa ba.
Sanata Barau I. Jirbin ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa rabon tallafin shinka ga al'ummar shiyyar Arewa maso Yamma. An ce an fara rabon tallafin a Kano.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar cafke wasu mata masu ba 'yan bindiga bayanai a jihar Kaduna. An cafke matan ne bayan sun je siyayya a kasuwa.
Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta yi martani kan kalaman da Rabiu Musa Kwankwaso ya yi na cewa ta mutu. PDP ta ce Kwankwaso baya da tasiri a siyasance.
Gwamnatin jihar Benue ta kulle kamfanonin tsohon gwamna, Samuel Ortom kan zargin kin biyan haraji na makudan kudi inda wasu ke zargin bita da kullin siyasa ne.
An kawo jerin jami’an da suka ajiye mukaminsu, suka bar aiki a gwamnatin Bola Tinubu. Kafin shugaban NIA, Farfesa Abubakar Rasheed ya hakura da kujerar NUC.
Fasto Babatunde Elijah Ayodele ya shawarci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan ya rage kashe kudade a gwamnatinsa. Ya ce ya kamata ya tsuke aljihun gwamnati.
Sarkin Potiskum da ke jihar Yobe, Mai Martaba, Umar Bauya ya kai ziyarar goyon baya ga Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II a jihar inda ya roke shi alfarma.
Masu zafi
Samu kari