Latest
Wasu miyagun 'yan ta'adda da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne sun sake kai hari a jihar Neja. 'Yan ta'addan sun kai sabon harin ne a karamar hukumar Shiroro.
Yayin da ake jimamin mummunar ambaliyar da ta afku a Maidugurin jihar Borno, ruwa ya sake yin ɓarna a yankin ƙaramar hukumar Lere ta jihar Kaduna.
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA), reshen jihar Kano ta bayyana cewa an jirkita labarin 'yan takarar zaben kananan hukumomi mai zuwa.
Kungiyar malaman jami'a reshen jihar Gombe ta shiga yajin aiki kan gaza cika alkawarin gwamnati. Kungiyar ASUU ta ce gwamnatin Gombe ne ta jawo yajin aikin.
A wannan rahoton, gwamnatin jihar Yobe ta ba da sanarwar samun ambaliyar ruwa a kananan hukumomi tara na jihar sakamakon cikar dam din Dadinkowa da Lagdo.
Kasurgumin dan ta'adda, Bello Turji ya fitar da sabon bidiyo inda ya ke gargadin lauya, Bulama Bukarti da kuma tura sako ga Isa Pantami da Murtala Bello Asada.
Rahotanni sun nuna cewa wasu mazauna birnin Maiduguri sun fara komawa gidansu biyo bayan janyewar ruwan ambaliya da safiyar yau Laraba a jahar Borno.
Ambaliyar ruwa a Maiduguri ta kashe yan Boko Haram sama da 100 a dajin Sambisa. An ruwaito cewa ambaliyar ta haura maboyar Boko Haram ne yayin da suke barci.
A labarin nan, za ku ji cewa jam'iyyar NNPP reshen jihar Kano ta barranta yan takararta a zaben kananan hukumomi mai zuwa da amfani da miyagun kwayoyi.
Masu zafi
Samu kari