Latest
Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai hari caji ofis a jihar Anambra da ke Kudu maso Gabashin Najeriya, sun hallaka ƴan sanda 3 tare da tashin bama-bamai.
Ana zargin DSS da cin zarafin al'ummar Najeriya ba bisa ka'ida ba wanda ya zama ruwan dare kama daga mamayar ofishin SERAP zuwa cafke shugaban NLC, Joe Ajaero.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya iso birnin Maiduguri, babbak birnin jihar Borno domin jajatawa al'umma sakamakon ambaliyar ruwan da ta afku a makon jiya.
Kungiyar likitoci NMA reshen jihar Borno ta yi kora ga gwammatin Babagana Umaru Zulum ta ƙara zage dantse wajen ɗaukar matakan kare lafiyar jama'a Maiduguri.
Gwamna Abba Yusuf ya jaddada cewa Kano tana tare da jihar Borno a mawuyacin halin da ta ke ciki na ambaliyar da ta mamaye Maiduguri. Abba ya ba da tallafin N100m.
Hukumar kididdiga ta ƙasa (NBS) ta bayyana cewa an fara samun sauƙin farashin kayayyaki a Najeriya a watan Agusta, 2024 idan aka kwatanta da watan Yuli.
Jam’iyyar adawa ta APC a Kano ta bayyana cewa za ta sa ido kan yadda gwamnatin Abba Kabir Yusuf za ta yi amfani da tallafin gwamnatin tarayya a jihar.
A wannan rahoton, kungiyar Northern Elders Forum ta bayyana damu wa kan halin da jami'an rundunar sojin ruwa na kasa, Seaman Abbas Haruna ke ciki.
Matatar Dangote da kamfanin man Najeriya na NNPCL sun yi sabani kan yadda farashin mai yake a tsakaninsu. Dangote ya ce ba a Naira ya sayar da mai ba ga NNPCL.
Masu zafi
Samu kari