Latest
Jami'an tsaro na hukumar 'yan sandan farin kaya (DSS) sun samu nasarar hallaka 'yan bindiga mutum biyu tare da cafke wasu da ake zargi da dama a jihar Neja.
Matakai da duk abin da kuke da buƙatar sani kan yadda ake duba sakamakon jarabawar kammala sakandare ta NECO 2024. Ana iya dubawa a waya ko na'ura mai kwakwalwa.
Tsohon Ministan shari'a a mulkin Olusegun Obasanjo mai suna Kanu Agabi ya shawarci yan siyasa kan magudin zabe inda ya ce ka da su yi tsammanin taimakon Ubangiji.
Jigon APC a jihar Edo ya ce za su yi nasara a zabe mai zuwa a jihar Edo duk da wahalar rayuwa da ake fama. Ya ce ba Bola Tinubu ba ne ya kawo wahalar rayuwa Najeriya
Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki coci guda biyu a yankin ƙaramar hukumar Kajuru a Kaduna, sun hallaka mutane 3 tare da sace wasu akalla 30 ranar Lahadi.
An yi mummunan hadarin mota a jihar Ogun inda mutane 18 suka kone kurmus bayan motar ta kama da wuta. Matukin motar na kwance a asibiti saboda raunuka.
A wannan rahoton, za ku ji cewa Attajirin dan kasuwa, Alhaji Aminu Dantata ya ziyarci jihar Borno domin jajanta wa gwamnati da al'uma bisa iftila'in ambaliya.
Mazauna Filato sun kwana cikin bakin ciki bayan wasu mutane dauke da migayen makamai sun farmaki mazauna Mbar a karamar hukumar Bokkos da ke jihar Filato.
Dattawan yankin Gobir a jihar Sakkwato sun roki gwamnatin tarayya da ta jihar Sakkwato su taimaka su sa a ƙwato gawar marigayi sarki daga daji don masa janaza.
Masu zafi
Samu kari