Latest
Majalisar dinkin duniya ta sanar da cewa za ta bada tallafin Dala miliyan 6, kimanin N10bn a kudin Najeriya ga waɗanda ambaliya ta rutsa da su Maiduguri.
Asue Ighodalo ya ce Edo PDP za ta rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a lokacin da gwamnatin tarayya da ‘yan sanda suka saki 'yan jam’iyyar da aka tsare.
Ana kyautata zaton cewa mutuwar Halilu Sububu za ta takaita ayyukan ta'addanci a Arewacin Najeriya kasancewarsa mai safarar makamai da horar da 'yan bindiga.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka 'yan bindiga a jihar Kaduna bayan sun yi musayar wuta. Sojojin sun kuma ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya shawarci matasa da suka kammala samun horaswa a sansanin hukumar NYSC a jihar domin amfani da damar da suka samu.
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya ce jiharss na da wadataccen ruwan da zai kashe kowace irin wuta, ya ce watakila ya faɗi wasu kalamai da suka ɓata ran Wike.
Gwamnan jihar Anambra, Charles Chukwuma Soludo, ya kori kwamishinan yada labarai na jihar daga mukaminsa. Majiyoyi sun ce kwamishinan bai san makamar aiki ba.
Bankin CBN ya ce cire tallafin man fetur da matsalolin tsaro za su iya zama barazana ga tattalin arzikin Najeriya. CBN ya ce asusun wajen Najeriya zai iya ci baya.
A wannan labarin, kwanaki bayan tsere wa daga gidan yari da ke Maiduguri, yan sanda sun yi nasarar kama wani matashi da ya tsere daga kurkukun bayan ambaliya.
Masu zafi
Samu kari