Latest
Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ya je jaje jihat Borno, ya ba da gudummuwar N50m a tallafawa mutanen da ambaliya ta shafa.
Jam'iyyar PDP a jihar Sokoto ta yi Allah wadai da sake ware makudan kudi har N30bn na wasu ayyuka inda ta bukaci hukumar EFCC ta fara bincike a kai.
Uwargidan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, Sanata Oluremi Tinubu ta ba da gudunmawar N500m domin tallafawa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Borno.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya ja kunnen sarakunan Borno kan illar da ke tattare da hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba a jihar.
Kotun majistare a jihar Kano ta sake tasa keyar matashin dan jarida zuwa gidan gyaran hali na Kurmawa kan zargin cin mutuncin Gwamna Abba Kabir da Sanusi II.
Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya baro babban ofishin hukumar EFCC ta ƙasa da ke Abuja, ya ce jami'ai sun amince ya tafi ba tare da sun masa tambayoyi ba.
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya ba talakawan Maiduguri Naira miliyan 100 bayan ambaliyar ruwa. Gwamna Babagana Zulum ya mika godiya mai yawa.
Wata kungiyar dattawan jihar Zamfara ta shawarci gwamnan jihar Dauda Lawal da ya mayar da hankali wajen sauke nauyin da ke kansa maimakon sukar Bello Matawalle.
Rahotanni daga jihar Anambra a Kudu maso Gabashin Najeriya sun nuna wasu miyagu sun sace shugaban kauyen Abatete, High Chief Ezebinobi Ezeigbo ranar Talata.
Masu zafi
Samu kari