Latest
Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin tarayya ta dakatar da wasu manyan jami'ai 4 da ke aiki a hukumar kula da gidajen gyara hali na kasar kan zargin karbar rashawa.
Majalisar wakilan kasar nan ta shawarci gwamnatin tarayya ta umarci NNPCL ya sahalewa yan kasuwa su fara sayo fetur kai tsaye daga matatar Dangote.
Wata kungiyar matasa a jam'iyyar APC ta bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da karamin ministan tsaro, Bello Matawalle daga mukaminsa.
Olukemi Iyantan ta zama kwamishiniya a hukumar NPC. Majalisar dattawa ta ce Iyatan ta cancanci nadin ne saboda kasancewarta a matsayinta na aikin gwamnati.
Darajar kudin Najeriya ta kara faduwa a farashin gwamnati da kasuwar fayan fage ta ƴan canji ranar Laraba, 25 ga watan Satumba, 2024, Dala ta koma N1,9l680.
Gwamnatin Tarayya ta ware makudan kudi har N24bn domin tallafawa gidaje fiye da 900 a jihohin Najeriya 36 da birnin Tarayya, Abuja domin rage radadi.
Hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta bayyana adadin 'yan ta'addan da dakarun sojoji suka hallaka a cikin watanni uku. Sojojin sun kwato makamai masu yawa.
Gwamna Chukwuma Soludo na jihar Anambra ya ba ma'aikatan jiharsa tabbacin cewa daga watan Oktobar 2024 za su fara karbar sabon mafi karancin albashin N70000.
Shugaban jam'iyyar APC, Ganduje ya jagoranci gwamnonin APC zuwa fadar shugaban kasa, Bola Tinubu da ke Abuja a yau Alhamis 26 ga watan Satumbar 2024
Masu zafi
Samu kari