Latest
Wasu matasa sun gudanar da zanga zanga a sakatariyar jam'iyyar PDP da ke jihar Rivers. Masu zanga zangar sun nuna adawarsu da zaben da za a yi a jihar.
Barista Daniel Bwala ya magantu kan rade-radin yin garambawul a mukaman Ministoci inda ya bukaci yan Najeriya da su kara hakuri Bola Tinubu zai yi abin da ya dace.
A wannan labarin, za ku ji cewa gwamnatin tarayya ta bayyana damuwa kan yadda ake samun karuwar talauci a Arewacin kasar nan duk da karuwar arzikin kasa.
Mataimakin gwamnan CBN ya zargi Emefiele da yaudarar Buhari yayin canza kudi a 2022. Ya ce ba a bi tsarin da Buhari ya fada ba yayin canza sabon kudin Najeriya.
Rahotanni sun nuna cewa akalla ƴan bindiga 20 ne suka bakunci lahira a lokacin da faɗa ya kaure tsakanin kungiyoyi biyu da safiyar ranar Laraba a Katsina.
Shugaban majalisar wakilai ta 10, Tajudeen Abbas ya fito ya gayawa duniya cewa ko kadan ba shi da ubangida a siyasance. Ya ba matasan Najeriya shawara.
Ma'aikatan jinya da ungozoma na jihar Kano sun yi barazanar tsunduma yajin aiki matuƙar gwamnati ta gaza yin wani abu game da buƙatunsu nan da kwana 15.
Yayin da ake shirye shiryen zaben kananan hukumomi a jihar Ribas, Gwamna Siminalayi Fubara ya ba ma'aikata hutun kwanaki biyu domin kowa ya koma gida.
Majalisar jihar Edo ta janye dakatarwar da ta yi ga mambobinta guda biyu a watan Mayun 2024 da ta wuce kan zargin neman tsige shugabanta da mukarrabansa.
Masu zafi
Samu kari