Latest
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote Aliko Dangote ya bayyana dalilin da ya sa Najeriya ke bukatar daina jinginar da danyen man da take hakowa domin karbar bashi.
A wannan rahoton za ku ji yadda kungiyar fafutuka ta Hezbollah ta bayyana cewa ana kara samun nasarori kan sojojin Isra’ila da ke kokarin kutsawa Lebanon.
An samu tashin wani abin fashewa a jihar Delta wanda ya yi sanadiyyar rasa rai. Wasu mutanen da lamarin ya ritsa da su sun samu raunuka inda aka kai su asibiti.
Ministan tsaro, Bello Matawalle ya ce za su canza salon yaki da yan bindiga wajen hana yan ta'adda yawo a jihohin Arewa. Matawalle zai ziyarci jihohin Arewa uku.
Farashin man fetur ya sake tashin gwauron zabi a Najeriya. Gidajen mai mallakar kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) sun kara kudin man daga N897 kan kowace lita.
Tun bayan kara tabarbarewar tsaro a Najeriya musamman a Arewacin kasar ake zargin wasu da hannu a harkokin ta'addanci da suka musanta lamarin a lokuta da dama.
Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa wasu masu zuba jari daga kasar Koriya ta Kudu za su gina matatun mai hudu da kowacce za ta iya tace ganga 100,000 a rana.
Yan sanda sun kama sarkin da yake taimakawa yan bindigar Arewa da bayanan sirri. An kama basaraken tare da sauran mutane da suke taimakawa yan bindiga.
Shugaban hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya bayyana cewa hukumar na kokari a samu ragi kan kudin aikin Hajjin shekarar 2025.
Masu zafi
Samu kari