Latest
Rundunar sojan sama ta Najeriya (NAF) ta fitar da ka’ida ga wadanda suka kammala karatu a manyan makarantu kuma suke da sha'awar shiga aikin sojan a bangaren DSSC.
A wannan labarin, za ku ji tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya sa wa shugaban kasa Bola Tinubu lakabin 'TPain' bayan an samu karin farashin fetur.
An samu gidajen man fetur da suke sayar da mai a kasa da farashin kamfanin NNPCL a birnin tarayya Abuja. Gidajen man suna yi wa mutane sauki duk da karin kudin fetur
Uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu ta ce ba mijinta, Bola Tinubu ne ya jefa 'yan Najeriya a mawuyacin hali ba. Ta ce nan da shekaru biyu komai zai canja.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya amince da fara biyan ma'aikatan jihar sabon mafi karancin albashi. Gwamna Zulum ya sa lokacin fara biya.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Filato (PSIEC) ta fara sanar da sakamakon zaben kananan hukumomin jihar inda ta ce PDP ta lashe kujeru 10 zuwa yanzu.
Shugaban kungiyar TUC, Festus Osifo ya roki gwamnatin tarayya da ta dawo da farashin man fetur kamar yadda yake a watan Yunin 2023, kusan N450 kan kowace lita.
Sojojin Najeriya sun harbe jagoran yan ta'adda da ake kira da Mai Hijabi a jihar Jigawa. Haka zalika sojojin Najeriya sun kashe miyagu da yan bindiga a jihohi.
Majalisar Tarayya da ke birnin Abuja ta tabbatar da Dakta Badamasi a matsayin shugaban hukumar NSIPA a yau Alhamis 10 ga watan Oktoban 2024 yayin zamanta.
Masu zafi
Samu kari