Latest
Rundunar yan sanda a Lagos ta wanke jarumar fina-finai, Lizzy Anjorin -Lawal kan zargin satar zinari da ake yi mata a kasuwar Oba Akintoye inda ta ce an yi kuskure.
Tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Kalu ya ce yana kwarewar zama shugaban ƙasa kuma da yiwuwar ya nemi takara idan Bola Tinubu ya hakura da neman tazarce.
Dubun wani dan bindiga da ya kashe yan mata a jihar Ogun ta cika. An kama dan bindigar ne bayan ya kashe yan mata ya wulakanta gawarsu a wani yanki na Ogun.
Wasu yan bindiga sun kai hari a jihar Katsina a yau Juma'a 18 ga watan Oktoban 2024 inda suka sace shugaban jam'iyyar APC a yankin karamar hukumar Sabuwa.
Gwamnatin jihar Kaduna ta sanya dokar takaita zirga zirga a fadin jihar daga karfe shida na safe zuwa karfe 7 na yamma a ranar Asabar, 19 ga Oktobar 2024.
Jami’an ‘yan sandan jihar Bauchi sun kama wasu daliban makarantar sakandare biyu bisa zargin satar wayoyin hannu guda 100 da na’urorin lantarki a wani shago.
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi ya bayyana damuwa a kan yadda kasar nan ke tafiya babu shugabanta ko mataimaki a fadar gwamnati da ke Abuja.
Hedkwatar tsaro ta ƙasar nan watau DHQ ta baygana cewa sojoji sun sheke ƴan ta'adda 96, sun cafke wasu sama da 200, tare da ceto mutanen da aka sace a mako 1.
Rundunar sojin Najeriya ta cafke mata da miji bisa zargin boye makaman yan bindiga a wani gida. Suna boyewa yan bindiga makami idan sun dawo daga kai hari.
Masu zafi
Samu kari