Latest
Wasu jiga jigan jam'iyyar NNPP a Kano da suka hada da Alhaji Auwalu Yusuf Dawakin Tofa sun sauya sheka zuwa APC ta hannun mataimakin shugaban majalisar dattawa.
Shugaban NNPP na kasa, Ajuji Ahmed ya gargadi jam’iyyar APC da cewa za a yi zaben Ondo bisa cancanta da tabbatar da zabin jama’ar jihar a zaben 16 Nywamba.
Rundunar sojin saman Najeriya za ta samu sababbin jiragen yaki 50 domin cigaba da kai hare hare kan yan bindiga. Sojoji za su cigaba da luguden wuta kan yan ta'adda.
Sanata mai wakiltar Abia ta Arewa, Orji Kalu ya ce shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya na sane da halin da kasar nan ke ciki domin ya na shiga mutane.
Gwamnatin tarayya ta hannun ma’aikatar ayyuka za ta kawo sabon tsarin karbar haraji a kan titin Abuja zuwa Keffi da mayar da Keffi-Akwanga-Markurdi zuwa hannu biyu.
Dan majalisar wakilan kasar nan ,Godwin Offiono ya kusa cimma muradinsa da samun amincewar majalisar ta kirkiro sabuwar jiha a shiyyar Kudu maso Kudu.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya kafa tarihi a Jihar Jigawa inda ya fara dura jihar domin mika tallafin N100m ga wandanda tankar mai ta kona a garin Majiya.
Aliko Dangote wanda ya samu karayar arziki tun daga shekarar da ta gabata ya sake zama mafi arziki a Afirka. Arzikinsa ya karu da $15bn zuwa Oktobar 2025.
Majalisar dattawan Kenya ta kada kuri'ar tsige mataimakin shugaban kasar, Rigathi Gachagua kan cin hanci da rashawa da wasu tuhume tuhume 10 da ya musanta.
Masu zafi
Samu kari