Latest
Yan sanda sun tarwatsa wasu matasa da ke kokarin kawo cikas a zabukan kananan hukumomi da ake cigaba da yi a ofishin hukumar zaben jihar Kaduna a yau Asabar.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai da ba a san ko su wanene ba sun hallaka dan takarar shugaban kasa a kasar Mozambique. Sun kuma hallaka lauyan 'yan adawa.
Tsohon gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom ya ce babu wani rabuwar kai a jam'iyyar PDP ta ƙasa, Umar Damagum ne shugaban kwamitin gudanarwa watau NWC.
An dakatar da kwamishinan ayyuka a jihar Jigawa bisa zarginsa da aikata aikin assha da matar aure a Kano. An kama shi ranar Juma'a a jihar ta Kano.
Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo ya kauracewa bikin Ofala na gargajiya da ake yi kowace shekara a birnin Onitsha saboda bunkasa al'adu.
Wani direban mota ya ce a yanzu ya koma sayen gas din CNG na N7,000 a rana a madadin N30,000 da yake kashewa don sayen man fetur a aikinsa na tuki.
Mutanen jihar Kaduna sun yi biris da dokar hana fita da gwamnatin jihar ta sanya domin zaben kananan hukumomin da ake gudanarwa a ranar Asabar, 19 ga watan Oktoba.
Wasu yan siyasa masu ƙarfin fada a ji a yankin Arewacin Najeriya suna kokarin neman yardar Jonathan domin tsayawa zabe a 2027 saboda dakile Bola Tinubu.
gwamnatin Najeriya ta ce za ta yi duk mai yiwuwa don hana malaman jami'o'i tafiya yajin aikin da suke shiri, ta ce ba za ta bari a rufe azuzun jami'o'i ba.
Masu zafi
Samu kari