Latest
Hukumar zaben jihar Kogi (KSIEC) ta sanar da zaben kananan hukumomi 21 da aka gudanar a jiya Asabar 19 ga watan Oktoban 2024 inda ya ce APC ce ta yi nasara.
Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq ya amince a fara biyan ma'aikatan gwamnatinsa sabon albashi mafi ƙaranci na N70,000 a watan Oktoba, 2024.
Shugaban gwamnonin Arewa, Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya jajantawa al'ummar jihar Jigawa kan iftila'i da ya afku inda suka ba da gudunmawar N900m.
Za a ga sunayen mutane 23 da aka zaba a APC a matsayin ciyamomi a jihar Kaduna. A cikin kananan hukumomi 23 da ake da su a jihar Kaduna, mace 1 tayi nasara.
Mun kawo ‘yan siyasar da za su iya ƙalubalantar Bola Tinubu idan zai nemi tazarce. Wasu sun fara kawo zancen wadanda za su nemi mulki a zaben 2027.
Tsohon gwamnan jihar Rivers ya bayyana kadan daga koma bayan da Atiku ya samu a siyasa, inda yace sam ba zai samu shiga ba a siaysar Najeriya saboda wasu dalibai.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon shugaban Najeriya, Janar Yakubu Gowon murnar cika shekaru 90 inda ya ce yana ba shi shawarwari masu kyau.
Wata budurwa 'yar shekaru 19 ta kammala digiri, inda ta samu maki mafi girma a tsangayar da ta ke karatu, jama'a sun taya ta murna tare da mata fatan alheri.
Wasu yan bindiga sun tarwatsa taron jam'iyyar LP a jihar Abia inda suka yi garkuwa da jiga-jiganta ciki har da mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa.
Masu zafi
Samu kari