Latest
A Najeriya ana karrama mutanen da suka ba da gudunmawa wajen ci gaban kasa da lambobin yabo na kasa. Wannan karramar ta kan shafi 'yan kasashen waje.
Wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da wata mai yi wa kasa hidima (NYSC) a jihar Neja. 'Yan bindiga sun sace matashiyar ne lokacin da take kan hanya.
Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede ya kori jami'ai da aka kama da laifin cin hanci da rashawa. Shugaban ya ce za a cigaba da korar wadanda aka kama da laifi.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya miƙa sunayen mutum 3 da ya naɗa a matsayin RECs na hukumar INEC ga majalisar dattawan Najeriya domin tantance su.
Jam'iyyar PDP mai adawa a jihar Ondo ta yi watsi da sakamakon zaben gwamnan jihar wanda APC ta lashe. PDP ta ce za ta garzaya zuwa kotu domin kalubalantarsa.
A wannan rahoton kun ji cewa jm'iyyar adawa ta PDP ta shiga yanayi mara dadi bayan zargin wasu jami'an hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta sako ta a gaba.
Majalisar Dattawa ta sadaukar da zamanta na yau Talata 19 ga watan Nuwambar 2024 domin yin bankwana da gawar Sanata Ifeanyi Ubah a birnin Tarayya Abuja.
Kasar Iran ta ƙaryata zancen cewa shugaba Ayatullah Ali Khamenei yana kwance rai a hannun Allah. Iran ta ce shugaba Ayatullah Ali Khamenei na nan lafiya kalau.
Shugaban jam'iyyar NNPP na jihar Osun, Tosin Odeyemi, ya caccaki Abdullahi Umar Ganduje kan kalaman da ya yi dangane da kalaman da ya yi kan zaben Ondo.
Masu zafi
Samu kari