Latest
Rundunar yan sanda a jihar Kano ta kama hatsabibin dan dabar unguwar Ɗorayi da ake nema ido rufe. An kama Auwal ɗan daba ne bayan an dauki lokaci ana nemansa.
Kamfanin mai na ƙasa watau NNPCL ya tabbatar da cewa matatar man gwamnatin tarayya da ke Fatakwal, babban birnin jihar Rivers ta fara aiki kan ɗanyen mai.
Yayin da ake zargin malamai da ci da addini, Sheikh Kabiru Gombe ya yi magana kan lamarin inda ya ce Bola Tinubu da Kashim Shettima sun fi kowa ci da addini.
Sanata Enyinnaya Abaribe, mai wakiltar Abia ta Kudu, ya yi ikirarin cewa majalisar tarayya ba ta ba Tinubu izinin sayen sabon jirgin shugaban kasa ba.
Gwamna Abba Kabir Yusuf zai kara tura daliban jihar Kano karatu kasashe waje. An kafa kwamitin da zai tantance ya'yan talakawan Kano domin tafiya karatu waje.
Gwamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu ya fusata kan rubutun da daya daga cikin hadimansa ya yi musamman game da zanga-zangar EndSARS a shekarar 2020.
A ranar Laraba, 27 ga watan Nuwambar 2024 ne ake sa ran Shugaba Bola Tinubu zai gabatar da kasafin Naira tiriliyan 48 na 2025 gaban majalisar tarayya.
Jam'iyyun adawa da dama a Najeriya sun shirya yin wata irin haɗaka mai ƙarfi domin tunkarar zaben 2027 da kuma kifar da Bola Tinubu duba da tsare-tsarensa.
Jami'ar jihar Taraba ta shiga jimami sakamakon rasuwar manyan malamanta har guda uku a tsakanin abin da bai wuce kwanaki uku ba, ma'aikata suɓ fara fargaba.
Masu zafi
Samu kari