Latest
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya gargadi wasu sanatoci inda ya sha alwashin tube duk wani shugaban kwamiti da ya gaza yin abin da ake tsammani.
Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) reshen jihar Kaduna ta dakatar da yajin aikin da ta fara kan sabon mafi karancin albashi. Ta dakatar da yajin aikin na sati daya.
Tsohon shugaban kungiyar kwadago reshen jihar Edo, Comrade Kaduna Eboigbodin, ya rasa ransa jim kaɗan bayan wata yar hatsaniya da yan sanda a Benin.
Afrika ta Kudu na son kara dangon alaka da Najeriya. Shugaban kasar, Cyril Ramaphosa ya fadi abin da su ke fata. Ya nemi a zuba jari a cikin kasarsa.
Dakarun sojojin saman Najeriya sun kai hare-hare kan sansanonin 'yan ta'adda a jihar Zamfara. Sojojin sun hallaka da yawa daga cikin masu tayar da kayar bayan.
wata gobara da ta kama sakamakon haɗuwar motar katifa da wayar wutar lantarki ta babbake kayan maƙudan kudi a wata kasuwa a Ilorin a jihar Kwara.
Gwamnatin jihar Neja ta fito ta yi magana kan rahotannin da aka rika yadawa dangane da batun 'yan bindiga sun kai farmaki kan ayarin motocin Gwamna Umaru Bago.
Shugaba Bola Tinubu ya yi umarni a saurari kofare kofaren jama'a kam ƙudirin haraji da ke gaban majalisar tarayya. Ya ce ba za a cuci Arewa kan kudirin haraji ba.
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III, ya bukaci 'yan Najeriya da su rika taimakon mabukata da dukiyoyinsu. Ya ce dukiya ba ta da tabbas.
Masu zafi
Samu kari