Latest
Wasu daga cikin 'yan majalisar wakilai na jam'iyyar LP sun sanar da sauya shekarsu zuwa APC. 'Yan majalisun sun yi bankwana da LP a ranar Alhamis.
Yan ta'adda sun dasa bama-bamai a garin Dansadau da ke karamar hukumar Maru a Zamfara inda yan sanda suka zargi kungiyar Lakurawa da alhakin kai harin.
EFCC ta gabatar da shaida a farko a kan zargin tsohon gwamnan Kwara da almundahana. Ana zargin AbdulFatah Ahmed da almubazzarancin N5bn na inganta makarantu.
Rundunar 'yan sandan jihar Akwa Ibom, ta samu nasarar bankado wata masana'antar kera bindigogi. Ta cafke daga cikin mutanen da ake zargi kan lamarin.
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya bayyana cews ko alama ba jihar Legas ce za ta fi amfana da sabon kudirin dsuya fasalin harajin shugaba Boa Tinubu ba.
Mataimakin gwamnan Borno, Dr. Usman Kadafur ya tsallake rijiya da baya. Jirgin Max Air da ya dauko shi da wasu fasinjoji 70 ya samu matsalar inji.
Malamin jami'ar Uyo, Inih Ebong ya samu nasara a kotu bayan fafutkar shekaru 22 yana zuwa kotuna. Kotu ta umarci a biya shi hakkokinsa na shekarun.
Sheikh Murtala Bello Asada ya yi magana kan alakar Shugaba Bola Tinubu da kasar Faransa inda ya ce hakan ya fi sabon kudirin haraji masifa a Najeriya.
Kwamitin majalisa ya fara shirin warware matsalolin da ke kunshe a kudirin haraji. Ana sa ran fara tattaunawa da babban lauya na kasa, Lateef Fagbemi.
Masu zafi
Samu kari