Latest
Rundunar 'yan sanda sun yi kare jini biri jini da 'yan bindiga a jihar Imo. An kashe 'yan sanda biyu yayin da aka kashe yan bindiga uku aka kama wasu miyagun.
Gwamnan jihar Jigawa ya shiga jimami bayan rasuwar mahaifiyarsa a yau Laraba. Za a yi jana'izar Hajiya Maryam Namadi a yau Laraba a Kafin Hausa karfe 4:30.
Ali Nuhu ya gargadi jaruma Rayya kan yunkurin da take yi na zana tattoo. 'Yan Kannywood da dama sun mara masa baya, suna neman ta dakatar da wannan shiri.
Rundunar 'yan sanda ta samu gagarumar nasara a kan wasu 'yan ta'adda a jihar Anambra. An kama boma bomai 19 a maboyar yayin da aka harbi wasu da dama.
An yi kazamin fada tsakanin 'yan ssanda da 'yan bindiga a Katsina inda aka ceto mutum 10 amma biyu sun mutu. Rundunar ‘yan sanda tana cigaba da bincike kan lamarin.
Gwamnatin jihar Jigawa ta kulla yarjejeniyar noma da kamfanin China domin inganta noma. Za a yi amfani da kayan noma na zamani domin yaki da yunwa da talauci.
Wani barawon kayan wutar lantarki ya hadu da mugun tsautsayi inda wuta ta babbaka shi ya mutu har lahira yayin satar kayan wuta a jihar Enugu. Wuta ta kona shi sosai
Masu garkuwa da mutane sun kashe wani yaro dan shekara 10 Tasi’u Abdullahi a Filato duk da karbar kudin fansa. An rahoto cewa an gano gawarsa ne a cikin buhu.
Jam'iyyar PDP ta kalubalanci Bola Tinubu da ya tafi daga Abuja zuwa Legas idan har tsaro ya inganta a Najeriya. PDP ta ce tsare tsaren Tinubu sun kawo wahala.
Masu zafi
Samu kari