Latest
Allah ya yiwa mahaifiyar marigayi Ahmad S Nuhu rasuwa. Shugaban hukumar fina finan Najeriya, Ali Nuhu ya sanar da lokacin da za a yi mata jana'iza a Jos.
Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta fitar da rahoto kan nasarorin da ta samu a 2024, ta kama 'yan daba, 'yan fashi da masu garkuwa da mutane da karin mutane 2,425
Wasu miyagun 'yan bindiga sun yi wa motar fasinjoji kwanton bauna a jihar Zamfara. 'Yan bindiga sun ta sa keyar dukkanin fasinjojin zuwa cikin daji.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya zama daya daga cikin shugabannin duniya da ake yi wa kallon kwararru a iya shirya wa da aikata rashawa a shekarar 2024.
Hukumar Hisbah ta cafke yara akalla 220 da ke gararamba a titunan jihar, inda aka gano sun fito daga jihohi akalla 14, daga ciki har da jamhuriyar Nijar.
Sojojin Najeriya sun kashe wasu manya manyan shugabannin ‘yan bindiga da suka hada da Halilu Sububu a karkashin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2024.
Rundunar 'yan sandan jihar Borno ta samu nasarar cafke wani jami'in CJTF mai taimakon 'yan ta'addan Boko Haram. Ya amsa laifin da ake zarginsa da shi.
Zainab Ado-Bayero ta yi barazanar kawo karshen rayuwarta sakamakon wahalar rayuwa da rashin tallafi tun bayan rasuwar mahaifinta, tsohon sarkin Kano.
Gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, ya nada sabon shugaban ma'aikatan fadar gwamnati. Gwamnan ya kuma raba wasu mukaman guda biyu a gwamnatinsa.
Masu zafi
Samu kari