An Yi Harbe Harbe a Kusa da White House da Trump ke Zaune

An Yi Harbe Harbe a Kusa da White House da Trump ke Zaune

  • Wani mutum ya mutu, yayin da wasu mutum hudu suka jikkata bayan wani dan bindiga ya bude wuta a Washington DC
  • Jami’an tsaro sun ce wanda ake zargin ya mutu bayan ya killace kansa a wani gida, inda ya yi musayar wuta da ‘yan sanda
  • Rundunar ‘yan sanda ta ce tana ci gaba da bincike domin gano musabbabin harin da kuma cikakken bayanin abin da ya faru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Washington DC – Mutum daya ya mutu, wasu mutum hudu kuma suka jikkata bayan wani dan bindiga ya bude wuta a cikin wani dakin motsa jiki da ke ginin gidajen haya a unguwar Logan Circle da ke birnin Washington DC na Amurka.

Lamarin ya faru ne a safiyar ranar Alhamis, a wani yanki da ke da tazarar kusan mil daya, wato kilomita 1.6, daga fadar White House.

Kara karanta wannan

An yi arangama da 'yan daba suka kai hari wurin taron magoya bayan Obi da Kwankwaso

Washington DC Amurka
Wajen da aka yi harbin bindiga a Washington DC Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton da BBC ta fitar ya bayyana cewa wanda ake zargin ya mutu bayan jami’an ‘yan sanda sun kutsa cikin gidan da ya killace kansa.

Mutum daya ya mutu

Jami’an tsaro sun tabbatar da mutuwar mutum daya, yayin da wasu hudu suka samu raunuka sakamakon harin.

Daya daga cikin wadanda suka jikkata na cikin mawuyacin hali, yayin da sauran ukun suka samu raunuka da ba sa barazana ga rayukansu.

Rahotanni sun nuna cewa harin ya fara ne a cikin dakin motsa jiki da ke ginin gidajen haya, inda mutane suka rika neman mafaka bayan jin karar harbe-harbe.

Wanda ake zargin ya bude wuta

Mukaddashin shugaban rundunar ‘yan sandan birnin Washington DC, Jefferey Carroll, ya bayyana cewa wanda ake zargin ya killace kansa a wani bangare na ginin bayan jami’an tsaro sun kewaye shi.

Carroll ya ce wanda ake zargin ya harbi jami’an tsaro ta kofar gidan a kalla sau biyu yayin da yake cikin gidan.

Kara karanta wannan

Kwana 2 kafin ziyarar Tinubu, 'yan bindiga sun kewaye gari sun buɗe wa mutane wuta

Ya kara da cewa jami’an sasanta rikici sun shafe wani lokaci suna tattaunawa da shi ta waya, amma daga bisani suka ji karar harbi, sannan ya daina amsa kiransu.

Daga nan ne jami’an ‘yan sanda suka kutsa cikin gidan, inda suka tarar da shi da raunin harbin bindiga da ake kyautata zaton shi da kansa ya yi.

Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Rahoton NBC ya nuna cewa Carroll ya kuma ce akwai alamun an kunna wuta a wurin, amma jami’an kashe gobara sun shawo kan lamarin.

Ya bayyana cewa hukumomi na ci gaba da bincike domin gano yadda abubuwan suka faru, dalilin harin da kuma abin da ya jawo rikicin.

An mika dan Najeriya Amurka

A wani labarin, mun ruwaito cewa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin mika Temitope Omotade zuwa Amurka domin fuskantar shari’a kan zargin damfara.

Mai shari’a Peter Lifu ya ce Ministan Shari’a na Tarayya ya gabatar da hujjojin da suka gamsar da kotu kan bukatar mika shi ga hukumomin Amurka.

Sai dai Omotade ya musanta zargin da ake masa, inda ya bukaci kotu ta yi watsi da bukatar mika shi, tare da bayyana cewa yana fama da matsalar hanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng