Latest
Shugaba Akufo-Addo na kasar Ghana ya dakatar da jawabinsa na ƙarshe kan yanayin ƙasa don tabbatar da cewa an kula da lafiyar mai tsaronsa wanda ya fadi.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu zai tafi ziyarar kwana ɗaya a jihar Enugu gobe Asabar, zai kaddamar da wasu muhimman ayyuka da Gwamna Mbah ya gama.
Kungiyar matasa da ke goyon bayan Atiku Abubakar watau NYFA ta caccaki Rabiu Kwankwaso kan kalaman da ya yi kan tsohon mataimakin shugaban ƙasar.
Shugaban kungiyar Izalah, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ba malaman Sunnah shawara kan rigimar Nijar da Najeriya inda ya ce ka da su manta da alakar Musulunci.
Kamfanin mai na kasa ya bayyana irin manyan nasarorin da ya samu ta fuskar farfado da matatun mai na Warri da Fatakwal, an fara gyaran ta Kaduna.
Kungiyar APC a shiyyar Arewa ta Tsakiya ta maida martani ga shugaban NNPP na Kano, Hashimi Dongurawa wanda ya ce Bola Tinubu ba zai kai labari ba a 2027.
Rahotanni daga rundunar yan sanda a birnin Tarayya Abuja sun tabbatar da cewa hukumar ta rasa jami'ai akalla 140 saboda yawan jini da ayyukan ta'addanci.
Fitaccen Fasto a Najeriya, Abel Damina ya jawo ka-ce-na-ce bayan ya yi magana kan haramcin shan sigari ko giya a addinance inda ya ce ba zunubi ba ne ko kadan.
Kamfanonin sadarwa a Najeriya sun yi koken cewa hauhawar farashi a kasar ya shafe su, saboda haka ne suke bukatar a sahale masu karin farashin waya.
Masu zafi
Samu kari