Latest
Babban Limamin Cocin RCCG, Pastor Enoch Adeboye, ya musanta hoton da ake yaɗawa na fasahar AI da ya nuna shi a matsayin Alhaji inda ya ce ba gaskiya ba ne.
Bishof Godwin Okpala wani fasto a cocin angilikan a Najeriya ya hadu da sharrin 'yan bindiga. Amma a karshe addu'a ta yi tasiri, limamin cocin ya shaki iskar 'yanci.
Daruruwan mutane ne suka yi dafifi domin gaishe da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, bayan sallame Sallar Juma'a a babban masallacin jihar Legas.
An samu tashin hankali bayan barkewar fadan Fulani da Manoma a jihar Jigawa. Mutane sun riga mu gidan gaskiya yayin da aka raunata wasu mutum hudu.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda wasu jagorori ke tsoma kansu wajen fitar da 'yan takara a Arewa.
AEDC ya ba mutane hakuri saboda za a gamu da matsalar wuta a Abuja. Gyare-gyaren da za a yi daga ranar 6 zuwa ranar 21 ga watan Junairun 2025 zai shafi unguwanni.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya amince da naɗin sababbin manyan sakatarori dindindin 45 a bangarori daban-daban na gwamnatinsa, ya kafa tarihi.
Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa an samu matsala tsakanin Sarkin Wase, Alhaji Muhammadu Sambo, da Wazirinsa, Muhammadu Badamasi a fada.
Rundunar 'yan sandan Jigawa ta kama wata amarya bayan saka guba a abincin ango da abokansa ana tsaka da ribibin biki. An kama amarya da wata mace daya.
Masu zafi
Samu kari