Latest
Gobarar dare ta halaka Jumai Sunday da ɗanta a Kugbo da ke Abuja. An gano gawarsu bayan kashe wutar, kuma 'yan sanda sun fara bincike kan lamarin.
Za a gudanar da zaben gwamnan Anambra a shekarar 2025. A cikin wannan rahoto, Legit.ng Hausa ta duba wasu dalilai biyar da ka iya hana Charles Soludo samun tazarce.
Reno Omokri ya bayyana yadda aka hana Muammar Gaddafi shigo da makamai Najeriya sau biyu karkashin mulkin Obasanjo, tare da rakiyar sojojinsa mata.
Babbar Kotun Tarayya da ke birnin Abuja, ta umarci Ministan Cikin Gida da Atoni-janar su bayyana gabanta cikin kwanaki uku kan tsarin haraji ga yan kasashen waje.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi magana kan zaben shekarar 2027. Gwamna Abba ya nuna cewa ko kadan batun sake komawa kan mulki ba shi a gabansa.
Gwamnatin Kano ta raba jarin Naira biliyan 2.1 ga mata a jihar Kano. Abba Kabir Yusuf ya ce an kawo shirin ne domin yaki da talauci da habaka tattalin arzikin Kano.
Jami'an tsaro a jihar Katsina sun samu nasarar hallaka gawurtaccen shugaban 'yan bindiga. Jami'an tsaron sun sheke shugaban 'yan bindigan ne a wani samame.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum ya ce babu wani abin alheri da za a yi wa sojojin da suka mutu a fagen fama da ya wuce taimakawa iyalansu.
Shugaban karamar hukumar Obio-Akpor a jihar Rivers, Hon. Chijioke Ihunwo ya nada hadimai na musamman guda 130 watanni shida bayan nada wasu 100 da ya yi.
Masu zafi
Samu kari