Latest
Rahotanni sun tabbatar an gano dan ta'adda Bello Turji da yaransa sun kwana suna dasa wasu abubuwa a kusa da duwatsun Fakai da Manawa don kare kansu daga hare-hare.
Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta ace ba ta da hurumin sauraron dukkanin korafe-korafen da suka danganci batun masarautu a kasar nan.
Gamayyar kungiyar fararen hula a Arewacin Najeriya sun fusata da yadda gwamnati ta kafe a kan tabbatar da kudirin harajin da ake ganin zai jefa jama'a a wahala.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bayyana cewa babu batun kutse a cikin asusun gwamnatin jihar Enugu har ta kai ga sace wasu biliyoyin Naira a baya-bayan nan.
Karamar ministar kwadago, Nkeiruka Onyejeocha ta ce gwamnatin Tinubu za ta sake duba mafi ƙarancin albashin ma'aikata nan da ƙasa da shekaru biyu masu zuwa.
Babbar kotun majistare da ke sauraron shari'ar tsohon jami'in gwamnatin jihar Kaduna, Muhammad Bashir Sa'idu ta haba belinsa biyo bayan tuhumarsa da almundahana,
Tsohon sakataren gwamnatin Kano, Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya bayyana cewa ya na da hujjojin da za su tona asirin wasu 'yan siyasa da ya ke zargi da cin amana
Gwamna Abba Yusuf ya saki N5bn ga masu fansho, ya kuma sanar da karin mafi karancin fansho zuwa N20,000. Abba ya ce Ganduje ya jefa 'yan fansho a cikin wahala.
Prince Adewole Adebayo ya ce Tinubu ya tarar da tattalin arzikin Najeriya cikin matsala, amma ya kara dagula shi saboda rashin kwararru a tawagarsa.
Masu zafi
Samu kari