Latest
INEC ta nemi Naira biliyan 126 maimakon Naira biliyan 40 da aka ware mata don gudanar da ayyukanta a 2025. Majalisar za ta tattauna magance matsalolin kuɗi na INEC.
Hukumar Shari’a ta Jigawa ta sallami ma’aikata uku tare da ladabtar da wasu alkalai saboda karya dokokin aiki, tana mai da hankali kan inganta gaskiya da adalci.
ACF ta yi bayani a kan rawar da ta ke takawa a wajen fitar da ɗan takara a zabukan kasar nan, inda ta nanata cewa dukkanin mambobinta na ajiye ra'ayin siyasarsu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da sashi na 26 na sabuwar dokar da ta haramta auren jinsi da lamarin yan daudu tsakanin sojojin Najeriya.
Wani matashin lauya a Kano yi maganar yiwuwar komawar Aminu Ado kan sarautar Kano. Lauyan ya yi fashin baƙin shari'ar da aka ba Muhammadu Sanusi II nasara.
Dattawan Kiristocin Najeriya sun caccaki Tinubu kan halartar taron Larabawa da kasashen Musulunci, suna masu zargin hakan ya saba wa kundin mulki.
Labari mai zafi ya zo mana cewa ana tunanin jami'an tsaron Najeriya sun sake yin kuskure. Wannan karo an saki bam da ya kashe mutane da dam dama a jihar Zamfara.
Sanata Orji Uzor Kalu da ke wakiltar Abia ta Arewa ya tarbi mutane sama da 8,000 da suka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC daga sauran jam'iyyun siyasa a jihar.
'Yan ta’addan Lakurawa sun kai hari a Kebbi, inda suka kashe mutane hudu, ciki har da ma’aikatan Airtel. Kwamishinan 'yan sanda ya nemi karin hadin kan jama’a.
Masu zafi
Samu kari