Latest
Wata kungiyar matasan Arewa sun bayyana rashin jin dadin yadda wasu daga cikin jagororin yankin su ke neman goyon bayan kudirin harajin Bola Ahmed Tinubu.
Hadimin shugaban kasa kan yada labarai, Daniel Bwala ya bukaci gwamnonin Arewa su rage surutu kan kudirin haraji su tura kukansu ga majalisar tarayya.
Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya ce babu wata tsamar siyasa tsakaninsa da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, gaskiya kawai yake ƙoƙarin gaya masa.
Gwamna Zulum ya yi Allah-wadai da kisan manoma 40 a Dumba, ya ja kunnen jama'a su zauna cikin yankunan tsaro don kare rayuwarsu daga barazanar 'yan ta'adda.
Gwamnatin jihar Borno ta nuna takaicinta kan harin da 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP suka kai a kan manoma. Ta bayyana harin a matsayin aikin ta'addanci.
M.A. Lawan ya bayyana cewa hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara bai tabbatar da dokar masarautun Kano ta 2024 ba, don haka har yanzu Aminu Ado Bayero ne sarkin Kano.
Rahotanni sun nuna cewa wani abin fashewa da aka bayyana a matsayin bom ya tarwatse a loƙacim da mutane ke tsakiyar barci da tsakar dare a jihar Imo.
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ba da shawara ga jihohin Arewacin Najeriya masu fama da matsalar rashin tsaro. Ya bukaci su yi koyi da tsarin da ya kawo.
NAHCON ta sanar da cewa gwamnati ta zabi jirage 4 don jigilar alhazai a aikin Hajjin 2025. Haka zalika, hukumar ta cimma yarjejeniya da kasar Saudiyya.
Masu zafi
Samu kari