Putin Ya Yi wa Ukraine Ruwan Wuta yayin da Wakilin Trump zai Shiga Kasar
- Hare-haren da Rasha ta kai a Ukraine cikin dare sun kashe mutane hudu tare da jikkata wasu, yayin da ake shirin fara sabon yunkurin sulhu tsakanin Moscow da Kyiv
- Wakilan Amurka Steve Witkoff da Jared Kushner, wanda kuma surukin Shugaba Donald Trump ne, na shirin ziyartar Moscow domin farfado da tattaunawar zaman lafiya
- Hare-haren sama tsakanin Rasha da Ukraine na kara tsananta yayin da dakarun kasashen biyu ke ci gaba da fafatawa a kan fagen daga mai tsawon kilomita 1,250
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kyiv – Hare-haren da Rasha ta kai a sassan Ukraine cikin daren Asabar sun kashe mutane hudu tare da jikkata wasu, yayin da Moscow da Kyiv ke jiran isowar wakilan Amurka domin sake farfado da tattaunawar neman kawo karshen yakin.
Ana sa ran Steve Witkoff da Jared Kushner za su ziyarci yankin domin kokarin farfado da tattaunawar zaman lafiya a tsakanin Rasha da Ukraine, bayan karuwar hare-haren sama da kasashen biyu ke kai wa juna.

Source: Getty Images
The Independent ta ruwaito cewa yakin sama tsakanin kasashen biyu ya kara tsananta ne yayin da dakarunsu ke fuskantar matsaloli wajen samun ci gaba a kan layin gaba da ya kai tsawon kilomita 1,250.
Rasha ta kai farmaki Ukraine
Hare-haren na Rasha sun zo ne duk da sakon da Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya wallafa ranar Juma'a, inda ya ce Ukraine za ta dakatar da hare-haren sama yayin ziyarar wakilan Amurka.
Zelenskyy ya kuma bukaci Moscow ta dauki irin wannan mataki domin samar da yanayin da zai ba wakilan Amurka damar gudanar da tattaunawar cikin kwanciyar hankali.
Ya ce Ukraine za ta tabbatar da tsaron sararin samaniyarta domin wakilan su isa lafiya, yana mai kira ga Rasha da ta guji kai hare-hare na tsawon lokacin da ake bukata domin gudanar da tattaunawar.
An kashe mutane 4 a Ukraine
Hare-haren Rasha sun kashe mutane hudu tare da jikkata wasu biyar a wani kamfanin masana'antu da ke yankin Dnipropetrovsk na kudancin Ukraine.
Shugaban gwamnatin sojin yankin, Oleksandr Hanzha, ya ce wani mutum mai shekaru 62 shi ma ya samu raunuka a wani hari daban da aka kai a gundumar Nikopol.
Rahoton AP ya nuna cewa ya bayyana cewa hare-haren sun kuma lalata wasu gidaje masu zaman kansu da kuma wani ginin gidaje.

Source: Getty Images
Trump ya kai hari Iran
A wani labarin, mun ruwaito cewa wani jirgin dakon man fetur na Iran ya fuskanci hari daga sojojin Amurka kusa da tsibirin Kharg, yayin da aka ji fashe-fashe da dama a yankin.
Rahotanni sun ce babu cikakken bayani nan take kan yanayin harin, irin barnar da aka yi ko kuma ko akwai asarar rayuka, yayin da hukumomin Amurka su ma ba su fitar da sanarwa ba.
Tsibirin Kharg na daga cikin manyan wuraren da Iran ke fitar da danyen man fetur, kuma a baya-bayan nan Amurka ta kai hari kan wasu na'urorin kare sararin samaniya a Iran.
Asali: Legit.ng

