Kasashe 10 mafi zaman lafiya a nahiyar Afrika

Kasashe 10 mafi zaman lafiya a nahiyar Afrika

- Kasar Najeriya ba ta samu shiga ba cikin sahun kasashe goma da za a ziyarta cikin kwanciyar rai a nahiyar Afrika

- Ruwanda da Bostwana su ne kasashe biyun farko mafi a Afrika mafi aminci da za a iya zuwa ba tare da dar dar ba saboda tsabagen zaman lafiya da ya wanzu a cikinsu

- Sauran kasashen da suka sami amincin kai musu ziyara ba tare da dar dar ba sun hadar har da Namibia, Ethopia, Lesotho da Zambia

A kididdigar da shafin Africa Facts Zone ya fitar dangane da kasashen da suka fi kowane aminci na zaman lafiya a shekarar 2019 da ta gabata, mun samu cewa kasar Rwanda ta ciri tuta.

A wallafar da shafin ya fitar da safiyar Juma'a, 19 ga watan Yuni kan shafin sada zumunta na Twitter, ya wallafa jerin kasashen Afrika 10 mafi zaman lafiya.

Cikin jerin da aka fitar, kasar Ruwanda ce ta jagoranci duka kasashen nahiyar yayin da Botswana, Mauritius da Namibia suka zo a mataki na biyu da na uku jere da juna.

Ba a bar kasar Morocco da Kenya a baya ba, inda su ma suka samu shiga cikin jerin da mataki na shida da kuma na goma.

Ga cikakken jerin kasashen 10 da matakin kowacce kamar haka:

1. Ruwanda

2. Botswana

3. Mauritius

4. Namibiya

5. Seychelles

6. Maroko

7. Habasha

8. Lesotho

9. Zambiya

10. Kenya

Kasashe 10 mafi zaman lafiya a nahiyar Afrika
Kasashe 10 mafi zaman lafiya a nahiyar Afrika
Asali: UGC

KARANTA KUMA: WHO ta ayyana Najeriya ta yi sallama da cutar shan inna

Hakazalika a baya bayan nan jaridar Legit.ng ta kawo muku jerin kasashen Afrika 14 masu 'yan sanda mafi kwarewa a kan aiki.

A kididdigar da Hukumar Kula da Sha'anin Tsaro da 'Yan sanda ta Duniya, World Internal Security and Police Index (WISPI) ta fitar, rundunar 'yan sandan kasar Bostwana ta fi kowace kwarewa a nahiyar Afrika.

A rahoton da WISPI ta fitar, ta yi amfani da binciken da Dr. Mamdooh Abdelmottlep ya gudanar kan rundunar 'yan sandan duk kasashen duniya.

Dr. Abdelmottlep wanda Farfesa ne kan sha'anin tsaro, shi ne shugaban kungiyar nazari kan jami'an 'yan sanda ta duniya, International Police Science Association.

Binciken ya nuna cewa, kasar Bostwana ce a kan sahu na farko a fannin sha'anin kwarewar rundunar 'yan sanda cikin kowace kasa a nahiyar Afrika.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng