Adam A Zango Ya Fitar da Sabon Faifan Bidiyo Kan Halin da Ya Ke Ciki, Ya Yi Godiya

Adam A Zango Ya Fitar da Sabon Faifan Bidiyo Kan Halin da Ya Ke Ciki, Ya Yi Godiya

  • A karshe, jarumi Adam A Zango ya fitar da wani sabon faifan bidiyo kan halin da ya tsinci kansa a ciki a yau Litinin
  • Zango ya bayyana cewa lafiyarsa kalau ba kamar yadda ake yadawa cewa ya shiga mugun yanayi da ka iya rasa rayuwarsa ba
  • Wannan na zuwa ne bayan wata wallafa da jarumin ya yi inda ya ke nuna mawuyacin hali da ya shiga a rayuwarsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Fitaccen jarumin fina-finan Kannywood, Adam A Zango ya fitar da sabon faifan bidiyo kan halin da ya ke ciki.

Zango ya fitar da faifan bidiyon ne yayin da ake ta cece-kuce kan halin da ya tsinci kansa a ciki.

Kara karanta wannan

Matawalle ya dauki zafi kan 'yan Arewa, ya kalubalanci wadanda Tinubu ya ba mukami

Adam A Zango ya fitar da bidiyo kan halin da ya ke ciki
Adam A Zango ya ce lafiyarsa kalau babu abin da ke damunsa kamar yadda ake yaɗawa. Hoto: adam_a_zango.
Asali: Instagram

Wani martani ya Adam Zango ya yi?

A cikin faifan bidiyon da ya karaɗe kafofin sadarwa, Zango ya ce shi dai lafiyarsa kalau kuma babu abin da ya ke damunsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jarumin ya yi godiya ga dukkan masoyansa da suke taya shi da addu'o'i duk da halin da ya shiga na damuwa.

Sai dai ya ce yadda ake yada lamarin kamar ya fara zaucewa ya wuce gona da iri kuma ba gaskiya ba ne.

Adam Zango ya yi godiya ga jama'a

"Assalamu alaikum jama'a ina godiya ga dukkan wadanda suka taya ni da addua'a da ba da shawara, nagode amma dai lafiya ta kalau babu abin da ya sameni."
"Saboda akwai wasu da ke wallafa kamar na zare ne ko na ruɗe ko kuma zan kashe kai na, lafiyata kalau babu abin da ya same ni."

Kara karanta wannan

"Za mu taimake shi": Ali Jita ya magantu kan halin da Adam A Zango yake ciki

"Tura ce kawai ta kai bango, kuma babu yadda za a yi ana aikomin hari ni kuma babu yadda zan mayar da martani, Nagode sosai da addu'o'i da kuma shawarwari."

- Adam A Zango

Ali Nuhu ya yi magana kan Zango

Kun ji cewa jarumi Ali Nuhu ya yi martani kan lamarin abokinsa, Adam A Zango da ake ta yadawa a kafofin sadarwa.

Ali ya ce lafiyar Zango kalau kuma babu abin da ke damunsa a halin yanzu inda ya godewa masoya kan addu'o'in da suke yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel