Barayi Sun Yashe Matashin Da Ya Tashi Daga Bauchi Zuwa Kano Don Ganin Jarumar Kannywood Aisha Humaira

Barayi Sun Yashe Matashin Da Ya Tashi Daga Bauchi Zuwa Kano Don Ganin Jarumar Kannywood Aisha Humaira

  • Wani matashi da ke matukar son jarumar Kannywood Aisha Humairah ya yi tattaki daga Bauchi zuwa Kano don ganinta
  • Sai dai Adamu ya gamu da ibtila'i inda barayi suka yashe shi tare da kwace duk wasu kayayyaki nasa
  • Ya kuma kamu da rashin lafiya inda rundunar yan sanda suka yi gaggawar kai masa agaji tare da kai shi asibiti

Jihar Kano - Wani matashi mai suna Adamu ya yi tattaki daga jihar Bauchi zuwa jihar Kano domin ya yi ido hudu da shaharriyar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood, Aisha Humaira.

Matashi da ya yi tattaki zuwa Kano don ganin Aisha Humairah ya hadu da ita
Barayi Sun Yashe Matashin Da Ya Tashi Daga Bauchi Zuwa Kano Don Ganin Jarumar KannyWood Aisha Hoto: Dokin Karfe TV Humaira
Asali: Facebook

Barayi sun sacewa matashin kayansa

Sai dai kuma, matashin ya hadu da sharrin barayi inda suka karbe masa komai a nan jihar Kano.

A wata hira da sashin Dokin Karfe TV ta yi da shi, matashin ya ce yanzu haka ya shafe kimanin tsawon kwanaki 15 a garin Kano domin ya ga jarumar saboda a cewarsa, wakokinta suna burgeshi.

Kara karanta wannan

"Fastoci Na Kwanciya Da Ita": Dan Shekara 84 Ya Kashe Matarsa Yar Shekara 75 Kan Rashin Bashi Hakkin Kwanciyar Aure

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An tattaro cewa a lokacin da isa garin Kano da jakar shi da tufafinsa masu kyau ya sauka, daga karshe aka sace komai nashi harda kudin shi ya dawo kwana duk inda ya samu.

A hirar da aka yi da shi ya ce iyayen shi sun san da zuwan nashi kuma sun mishi addu'ar Allah yasa ya ga jaruma Aisha Humaira.

Ya bayyana cewa suna zaune da iyayen shi a Bauchi dai-dai layin gidan kaura da ke GRA, kusa gidan baban Anas.

Yan sanda sun ceto Adamu

Sai dai kuma a halin da ake ciki, an tattaro cewa yaron ya fadi a kasa inda ya dunga fitar da farin ruwa, an kuma kwashe shi zuwa asibitin Murtala da ke nan a cikin garin Kano.

A halin yanzu, an tattaro cewa yan sanda sun samu nasarar kaiwa yaron agaji a inda ya ke kwance har ma sun kai shi Asibiti domin a ceto rayuwarsa.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Dan Adaidaita Ya Jera Tankunan Ruwa 13 a Kan Keke Ya Girgiza Intanet

Sun hadu da jaruma Aisha Humaira

Hakazalika, an ceita kanta A'isha Humaira ta samu labarin lamarin har ma ta tura wakilanta asibitin kafin daga bisani su da yaran za su gana.

Daga nan kuma an samu nasarar gano mahaifiyar yaron wacce aikin aikatau ta ke yi a wani gida a garin Bauchi biyo bayan rabuwa da uwar tayi da mahaifin yaron. Yanzu haka ma ta na hanyar zuwa Kano domin ta tafi da shi

Jama'a sun yi martani

Fahad Musa ya yi martani:

"Allah kashiryemu."

Musa Ahmad Shehu ya ce:

"Shirmen banza."

Hassana Muhammad Ungo ta ce:

"Masha Allah yasamu shiga."

Aliyu Idris ya ce:

"ALLAH ya kyauta ."

Musa Danjuma Bello ya ce:

"Naji dadi matuka da Allah yasa tasamu labarin har ta tura wakilanta domin duba lafiyarsa kafin su hadu."

Budurwa yar shekaru 20 ta ginawa kanta hadadden gida

A wani labari na daban, mun ji cewa wata kyakkyawar budurwa yar Najeriya ta cimma muradionta na gina gida da zama mai gidan kanta tun tana da kuruciyarta.

Matashiyar ta dauki hoto a gaban gidan da aka kammala gininsa tare da iyayenta yayin da ta kasance rike da takardun gidan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng