ECOWAS Ta Ce Bata Amince Sojojin Nijar Su Ci Gaba Da Mulki Har Shekaru 3 Ba

ECOWAS Ta Ce Bata Amince Sojojin Nijar Su Ci Gaba Da Mulki Har Shekaru 3 Ba

  • Kungiyar ECOWAS ta nuna rashin amincewarta da shirin sojojin Nijar na yin shekaru uku kan karagar mulki
  • ECOWAS ta ce kamata ya yi ace shugabannin sojin Nijar su mayar da hankali wajen yakar yan ta'adda, maimakon harkokin mulkin kasar
  • Tun farko dai shugaban mulkin soji, Janar Abdourahamane Tchiani, ya ce shekaru uku za su yi kan mulki sai su mika shugabanci ga farar hula

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kungiyar ECOWAS ta yi watsi da shirin sojojin juyin mulkin Nijar na mika mulki cikin shekaru uku masu zuwa, Daily Trust ta rahoto.

Kwamishinan harkokin siyasa, tsaro da tabbatar da zaman lafiya na ECOWAS, Abdel-Fatau Musa, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da sashin Hausa na BBC a ranar Lahadi, 20 ga watan Agusta.

Kungiyar ECOWAS ta ce bata yarda da mulkin soja na shekaru uku ba a Nijar
ECOWAS Ta Ce Bata Amince Sojojin Nijar Su Ci Gaba Da Mulki Har Shekaru 3 Ba Hoto: @ecowas_cedeao
Asali: Twitter

Janar Abdourahamane Tchiani, shugaban mulkin sojan Nijar, ya bayyana a wata sanarwa da ya yi a gidan talbijin a daren ranar Asabar, 19 ga watan Agusta, cewa rundunar soji za ta mika mulki ga gwamnatin farar hula cikin shekaru uku masu zuwa.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Shugaban Nijar Ya Bude Baki, Ya Fadi Shekarun da Zai Yi kan Mulki

Kamata ya yi ace sojojin Nijar na yakar yan ta'adda ba gwamnatin kasar ba, ECOWAS

Sai dai kuma, a cikin hirar da aka yi da shi, Abdel-Fatau Musa ya bayyana cewa bukatar Janar Tchiani dabara ce kawai don tattaunawa da diflomasiyya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma bayyana cewa ya kamata a ce shugabannin sojin Nijar sun mayar da hankali wajen yakar yan ta'adda, maimakon harkokin mulkin kasar.

Tawagar ECOWAS ta gana da sojin mulkin Nijar

Da farko dai tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar ya jagoranci wata tawaga ta ECOWAS zuwa Nijar a ranar Asabar a kokarin cimma matsaya ta zaman lafiya da sojin juyin mulki.

Tawagar sun hadu da Firai minista Ali Lamine Zeine wanda ya tarbe su a filin jirgin sama sannan ya jagorance su zuwa fadar shugaban kasar.

Kara karanta wannan

Aiki ja: Tawagar ECOWAS ta isa Nijar, ta samu ganawa da hambararren shugaba Bazoum

Daga bisani sun gana da hambararran shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum, bayan ganawarsu da Janar Abdourahamane Tchiani, shugaban mulkin soja.

ECOWAS dai na bukatar sojojin su mayar da hambararren shugaban kasar kan mulki ba tare da ɓata lokaci ba.

Shugaban sojin Nijar ya ce za su kare kansu

A gefe guda, mun ji a baya cewa Shugaban juyin mulkin jamhuriyar Nijar, janar Abdourahmane Tchiani, ya yi martani gameda shirin da ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS), take na kai mu su hari.

Tchiani ya bayyana hakan ne ranar Asabar, 19 ga watan Agusta kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel