Ahmed Musa Ya Gwangwaje Jarumi Abdullahi Karkuzu Da Kyautar Gidan N5,500,000

Ahmed Musa Ya Gwangwaje Jarumi Abdullahi Karkuzu Da Kyautar Gidan N5,500,000

  • Shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa Ahmed Musa, ya gwangwaje jarumi Abdullahi Karkuzu da kyautar gida
  • Ahmed Musa ya sayawa tsohon jarumin na Kannywood katafaren gida har na naira 5,500,000 a garin Jos
  • Hakan ya biyo bayan wani faifan bidiyo na jarumin da ya yaɗu a kafafen sada zumunta yana neman taimako

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jos, jihar Filato - Shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Super Eagles Ahmed Musa, ya gwangwaje jarumin fim ɗin Kannywood Abdullahi Shuaibu wanda aka fi sani da Karkuzu da katafaren gida.

Hakan ya biyo bayan wata hira da shafin Zinariya ya yi da Karkuzu a cikin bidiyo, wacce ta yaɗu sosai a kafafen sada zumunta.

Ahmed Musa ya yi wa Karkuzu gagarumar kyauta.
Ahmed Musa ya bai wa jarumi Karkuzu kyautar gidan naira 5,500,000. Hoto: Ahmed Musa MON, Zinariya
Asali: Facebook

Ahmed Musa ya sayawa Karkuzu gida na N5,500,000

Bayan ganin bidiyon ne Ahmed Musa ya ba da umarnin a nemo ma sa gida domin ya siyawa tsohon jarumin.

Kara karanta wannan

Hotuna Sun Bayyana Yayin Da Hadimin Buhari Ya Bayyana Inda Nasir El-Rufai Ya Koma Bayan Ya Hakura Da Zama Minista

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kamar yadda aka wallafa a shafin Zinariya na Facebook, Ahmed Musa ya gwangwaje Abdullahi Karkuzu da gida na naira 5,500,000 da ya saya ma sa a garin Jos.

An bayyana cewa gidan da aka sayawa Karkuzu gida ne matsakaici da ya ƙunshi jimillar ɗakuna guda biyar, ɗakin girki da kuma makewayi.

Baya ga wannan gida da Musanya sayawa jarumi Karkuzu, ya ba shi kyautar naira dubu 500 domin ya ciyar da iyalinsa.

Karkuzu ya nuna farin ciki da matuƙar godiya

Auwal Saleh Jos, mawallafin bidiyon da ya janyo hankalin Ahmed Musa, kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka jagoranci fafutukar nemowa Karkuzu gida, ya shaidawa Legit.ng irin halin farin cikin da jarumin ya tsinci kansa.

Ya bayyana cewa jarumi Karkuzu ya fashe da kukan daɗi, a yayinda aka ɗamƙa ma sa takurdun gidan da aka saya ma sa.

Kara karanta wannan

Hankalin Babban Gwamnan Jam'iyyar PDP Ya Tashi Bisa Zargin Yunkurin Yi Ma Sa Juyin Mulki

Auwal ya ƙara da cewa Karkuzu ya yi addu'a da nuna matuƙar godiyarsa da wannan abin alkhairi da Ahmed Musa ya yi ma sa. Haka nan ya godewa sauran al'umma da suka taimaka ma sa.

Jarumi Karkuzu dai ya kasance yana fama da ciwon makanta da kuma rashin abinda zai ɗauki ɗawainiyar iyalinsa gabanin samun wannan taimako.

Ahmed Musa ya sauke farashin fetur a gidan mansa

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan sauke farashin litar man fetur da fitaccen ɗan wasan ƙwallo Ahmed Musa ya yi a kwanakin baya.

Musa ya sauke farashin man zuwa N580 a duk lita domin ragewa 'yan Najeriya raɗaɗin da cire tallafin man fetur ya jefa su a ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng