Kannywood: Bidiyon dankararrun akwatinan lefe 16 da Bashir Maishadda ya yiwa amaryarsa Hassana

Kannywood: Bidiyon dankararrun akwatinan lefe 16 da Bashir Maishadda ya yiwa amaryarsa Hassana

  • Masana'antar shirya fina-finan Hausa za ta sake yin gagarumin biki na yayanta guda biyu
  • Za a daura auren Bashir Maishadda da amaryarsa Hassana Muhammad a ranar Lahadi, 13 ga watan Maris
  • Babban furodusan na Kannywood ya hadawa amaryar tasa wacce take jarumar fim akwatinan lefe na gani na fada har guda 16

Ana ta shagulgulan biki a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannwood, inda a makon da ya gabata aka daura auren manyan jarumai biyu wato Aisha Aliyu Tsamiya da kuma Hafsat Idris.

A yanzu kuma ana ta shirye-shiryen biki a tsakanin babban furodusa, Abubakar Bashir Maishadda da amaryarsa kuma jaruma, Hassana Muhammad.

Kannywood: Bidiyon dankararrun akwatinan lefe 16 da Bashir Maishadda ya yiwa amaryarsa Hassana
Kannywood: Bidiyon dankararrun akwatinan lefe 16 da Bashir Maishadda ya yiwa amaryarsa Hassana Hoto: realabmaishadda
Asali: Instagram

Za a daura auren Maishadda da Hassana a ranar Lahadi 13 ga watan Maris, a masallacin Murtala kamar yadda jarumin ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Ya rubuta a shafin nasa:

Kara karanta wannan

Babban dalilin da yasa na fara daukan bindiga, Bello Turji a zantawarsa da yan jarida

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Da Sunan ALLAH Mai Rahama Mai Jinkai. Tsira Da AMINCIN ALLAH su Kara Tabbata Ga Shugabanmu Annabi Muhammad (S.A.W).
"Ina Farin cikin gayyatar masoya Daurin Aurena. Wadanda kuma ba zasu sami damar zuwa ba, sai su tayamu da addu’a. NA gode ❤️❤️❤️❤️"

An hada lefe na gani na fada

Tuni dai abubuwa suka fara kankama na bikin domin har an kammala hada akwatinan lefe na gani na fada har guda 16.

Maishadda da kansa ne ya wallafa bidiyon lefen a shafin nasa, yana mai cewa:

“LEFENE 13 NE Da Gyaran UKU har.......❤️❤️❤️ Wayata 13 CE.
“Ranar Aurena ON 13 Ne Inn shaa ALLAH!!!
“Addu’arku nada matukar muhimmanci masoya ❤️❤️❤️❤️.”

Bidiyo da hotunan Jaruma Laila ta cikin shirin Labarina yayin da ta yi aure

A wani labari na daban, labari da ke bayyana da dumi-duminsa a safiyar Asabar din nan shi ne na auren jarumar shiri mai dogon zango na Labarina.

Kara karanta wannan

Yadda matan Gwamnoni su ka fusata mutane da suka kai wa Aisha Buhari ‘cake’ har Dubai

Mai bayar da umarni na shirin Labarina, Malam Aminu Saira ne ya wallafa bidiyo tare da taya jarumar murnar auren da ta yi a madadin kansa da kamfanin Saira Movies.

Kamar yadda wallafar da @aminusaira yayi ta bayyana:

"A madadi na da kamfanin sairamoviestv, muna taya 'yar uwa Maryam Waziri murnar auren da ta yi a yau, wato Juma'a. Allah ya ba su zaman lafiya, Allah ya ba su zuriya dayyiba. Muna taya ki murna, muna kewar ki Laila"

Asali: Legit.ng

Online view pixel