Kuyi hakuri, amma gaskiya na fadi: Sarkin Waka ya saki sabon bidiyo, ya yi sabon bayani

Kuyi hakuri, amma gaskiya na fadi: Sarkin Waka ya saki sabon bidiyo, ya yi sabon bayani

  • Naziru sarkin waka ya sake fitowa ya ba wa jama'a hakuri a kan furucin da ya yi game da halin da masana'antar Kannywood ke ciki
  • Sarkin waka ya ce shi bai yi da nufin lalatawa wani sana'arsa ba illa kawai ya fadi gaskiyar abun da ya sani ne
  • Ya kuma ce sun taba zama da Ali Nuhu da Falalu Dorayi kan yadda za a gyara lamuran masana'antar amma ya lura ba mai yiwuwa bane shi yasa ya ankarar da jama'a

Shahararren mawakin Hausa kuma jarumi a kannywood, Naziru Ahmad wanda aka fi sani da sarkin waka, ya ba jama’a hakuri a kan kalaman da ya yi halin masana’antar ke ciki.

Naziru ya bayyana cewa shi bai yi furucin don lalata sana’ar kowa ba illa kawai ya ce iya gaskiyarsa ya fada.

Kara karanta wannan

TY Shaban ya gasgata maganar Naziru, ya bukaci ya rantse bai taba neman wata jaruma da lalata ba

Jarumin a cikin sabon bidiyon da ya saki, ya ce shi bai yi don wani ya so shi ko don wani ya ki shi ba, cewa akwai bukatar ayi gyara ne shiyasa ya fada ma al’umman gari halin da ake ciki.

Kuyi hakuri, amma gaskiya na fadi: Sarkin Waka ya saki sabon bidiyo, ya yi sabon bayani
Kuyi hakuri, amma gaskiya na fadi: Sarkin Waka ya saki sabon bidiyo, ya yi sabon bayani Hoto: Leadership
Asali: UGC

Hakazalika ya ce ya taba zama da Ali Nuhu da shi Falalu A Dorayi domin kawo gyara a harkar amma abun ya ci tura.

Ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa:

“Ina so na dan bamu hakuri a takaice a kan wannan abu. Mutane musamman mutanen gari dan Allah ayi hakuri wallahi ban fadi wannan don bata wa wani sana’arsa ba, ko dan wani ya so ni ko dan wani ya kini ba.
“Duk na san za a samu wannan, duk wanda zai fadi gaskiya ya san abun da zai biyo baya. Toh wadannan duk da kowa yake tayi harda wanda zai kai ba yayi magana dalili ne, kun san idan zabe ya kai sai ka ga wanda bai kai ba ma ya zagi shugaban kasa, babu komai wannan duk Allah zai kula da shi.

Kara karanta wannan

Batun Ladin Cimma: Jarumin fim ya yi barazanar tona asirin Naziru Sarkin waka, da sauran furodusoshi

“Duk wanda ya yi sharri ya san me zai tarar, duk wanda ya yi alkhairi ma. Ni dai Allah ya sani har n agama wannan maganar ban kama sunan wani ba. Wanda na kama sunansu misali ne nayi.
“Ni kuma duk wanda ya kama sunana ya yi mun kazafi Allah na nan.ni dai na san gaskiyata na fada. Mutane ku yi hakuri amma wadanda na kama sunan su misali nayi ba wanda bamu taba zama da shi ba don gyaran masana’antar.
“Mun zauna da shi Alin mun zauna da Falalu a kan gyaran masana’antar amma na lura abun ba zai kai ga a gyara ba gara a ankarar da mutane. An yi da Ciroki, manyan jarumai sun fito suna neman taimako duk an yi da su, ana karyata su.”

Batun Ladin Cimma: Jarumin fim ya yi barazanar tona asirin Naziru Sarkin waka, da sauran furodusoshi

A baya mun kawo cewa furucin da dattijuwar jarumar Kannywood, Ladin Cima ta yi na cewar ba a taba biyanta manyan kudi ba a harkar fim ba hasalima N2,000 zuwa N5,000 ake bata yana ci gaba da tayar da kura a tsakanin manyan jaruman masana'antar.

Kara karanta wannan

Ladin Cima: Naziru sarkin waka ya yiwa Ali Nuhu da Falalu wankin babban bargo

A yanzu jarumi Nuhu Abdullahi ya fito ya soki mawaki Naziru Ahmad wanda aka fi sani da sarkin waka, cewa bai yi adalci ba wajen yiwa Ali Nuhu da Falalu Dorayi kudin goro bayan sun fito sun bayyana su ga abun da suke biyan jarumar.

A wata wallafa da yayi a shafinsa na Instagram, Abdullahi ya bayyana cewa da ace za su fito suyi magana da mutuncin su Naziru sai ya zube.

Asali: Legit.ng

Online view pixel