Ni ba Musulmi ba ne, amma na san Annabi Muhammadu shine mutumin da yafi kowa a duniya - Chicharito

Ni ba Musulmi ba ne, amma na san Annabi Muhammadu shine mutumin da yafi kowa a duniya - Chicharito

  • Duk wadanda suka sanshi sai dai su fadi alheri, nagarta da kuma kyawawan halayyarshi
  • Wadanda suka karanta tarihinshi a natse, suna yawan yabawa tare da jinjinawa irin rayuwar da yayi a duniya
  • Chicharito dan wasan kwallon kafa ne na kasar Mexico wanda ya bayyana Annabi a matsayin mutum mafi nagarta a duniya, duk da kuwa Kirista ne

Wadanda Suka sanshi ko suka karanta wani abu a kan shi, sun san irin albarkatacciyar rayuwar da yayi. An gano cewa ‘yan kwallo da sanannu a duniya na nuna mishi soyayya saboda tarihin shi da suka samu. Wanna ba kowa bane sai Annabi Muhammad SAW.

An turo shi ne zuwa ga mutane baki daya. Ba Annabin musulmai bane kadai, dukkan mutane ne za a musu hisabi da zuwanshi.

Wani babban dan wasan kwallon kafa daga kasar Mexico, Javier Hernandez Balcazar wanda aka fi sani da ‘Chicharito’ ya shiga sahun masoya Annabi. A daya daga cikin wallafar da yayi a shafinshi na tuwita, ya bayyana irin kaunar da yake wa manzon ta yadda ya ce shi ne mutum mafi nagarta a duk duniya.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Rishi Sunak Ya Zama Sabon Firayim Ministan Birtaniya

Chicarito
Ni ba Musulmi ba ne, amma na san Annabi Muhammadu shine mutumin da yafi kowa a duniya - Chicharito
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da Chicharito mabiyin Katolika ne, rayuwar Annabi ta matukar burgeshi har ya bayyana abinda ke ranshi.

Chicahrito ne dan kwallon kafa na farko a kasar Mexico da yayi wasa da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United. Ya halarci wasan gasar kwallon kafa ta duniya a 2010. An karamashi bayan da yaci kwallaye 7.

Abun farin ciki ne da jin dadi idan kaga wadannan mutanen suna karanta tarihin Annabi kuma sun bayyana kaunarsu gareshi. Allah ya kara tabbatar da mu cikin addinin musulunci da shiriya ta gaskiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Kara karanta wannan

Yadda Dan Kwallon Najeriya Ya Nutse Bayan Ceto Fasinjojin 5 A Hatsarin Jirgin Ruwa Da Ya Ritsa Da Su

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng