Alamomi 10 dake nuna mutum ya fara kamuwa da ciwon zuciya

Alamomi 10 dake nuna mutum ya fara kamuwa da ciwon zuciya

Ciwon zuciya na nufin gazawar zuciyar wajen aika jini ga sassan jiki kamar yadda sassan jikin ke bukata. Ciwon zuciya kan iya samo asali daga hawan jinin da ba a bashi kulawar da ta kamata ba.

Yanayin da kan iya saka mutum saurin kamuwa da ciwon zuciya sun hada da; Hawan jini, Kibar data wuce kima, yawan shan giya, tu'ammali da guba, cin abinci marar tsafta, gadon ciwon zuciya, karancin wasu sinadarai da sauran su.

Alamomi 10 dake nuna mutum ya fara kamuwa da ciwon zuciya
Alamomi 10 dake nuna mutum ya fara kamuwa da ciwon zuciya

Wadannan abubuwan guda 10 sune zaka fara ji a jikin ka idan zuciya ta fara samun matsala:

1. Numfashi sama-sama

2. Kake jin kan ka tamkar ba nauyi

3. Rashin jurewa motsa jiki

4. Tari; matsakaici ko mai tsanani

DUBA WANNAN: Labari da dumin sa: Ladoja ya janye daga takarar shugabancin jam'iyyar PDP, ya goyi bayan Adeniran

5. Numfashin dake bayar da sauti

6. Saurin gajiya

7. Daukewar jin yunwa

8. Kumburin fuska da kafafu

9. Wahalar shakar numfashi yayin kwanciyar ruf da ciki

10. Faduwar gaba ko saurin bugawar zuciya

Masana harkar Lafiya na yawan shawartar jama'a da suke zuwa asibitoci domin yin gwaje-gwajen tabbatar da lafiyar su, ba sai sun ji basu da lafiya ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel