Ma’aurata 7 Sun Hada Bikinsu Don Ragewa Juna Zafin Kashe Kudi, Hotunan Sun Yadu
- Wasu ma'aurata bakwai daga gundumar Machakos sun gudanar da bikin aure na hadin gwiwa don ragewa juna zafi, suna masu nuni ga matsin rayuwa da ake ciki
- Sabbin ma'auratan sun kasance dauke da murmushi a fuskokinsu yayin da aka yi shagalin bikinsu sannan sun taka rawar murna kafin suka raba kek
- Jama'a sun yaba ma masoyan a kan wannan mataki da suka dauka, inda suka karfafa ma sauran jama'a gwiwar yin koyi da su maimakon cin bashi don yin biki
Masu bauta a cocin All Saints Kyamwee Anglican da ke gudunmar Machakos sun halarci wani biki na musamman da ya hada ma'aurata bakwai.
Me yasa ma'auratan suka yi auren hadin gwiwa?
A cewar NTV, ma'auratan sun ce sun yarda su yi biki na hadin gwiwa domin ragewa juna zafi saboda tsadar rayuwa da ake ciki.
Cocin ya cika makil da yan uwa da abokan arziki da kuma yan cocin da suka hallara domin shaida daurin auren masoyan.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ma'auratan sun hallara a coci daya bayan daya yayin da suka baje kolin rawansu masu kayatarwa.
Ma'auratan sun dauki alkawarin aure daya bayan daya sannan suka ciyar da junansu kek da hannayensu.
Daya daga cikin angwanan, Alphonse Mwaziri mai shekaru 74 ya bayyana cewa ya auri kyakkyawar matarsa tsawon shekaru 50.
"Ina zaune da matata cikin farin ciki. Ina rokon wadanda suke cikin zuriyata da su yi koyi da su kuma su yi aure a coci," in ji shi.
Joseph Mutungi, faston da ya daura auren ma'auratan guda bakwai, ya shawarci sauran mutane cewa:
"Kada ku ji tsoron yin aure a coci saboda babu banbanci tsakanin auren coci da na lambu."
Bayan shekaru 3 a Turai, yar Najeriya ta dawo ga saurayinta bakanike
A wani labarin kuma, mun ji cewa wani bakaniken bakin hanya mai suna Segun, ya cika da farin ciki yayin da budurwarsa, wacce ya dauki nauyin karatunta zuwa kasar Birtaniya ta dawo bayan shekaru uku.
Wani mai watsa shirye-shirye a TikTok Theo Ayoms, wanda ya taimaka wajen sake hada su, ya wallafa bidiyon mai tsuma zuciya a soshiyal midiya.
Asali: Legit.ng