An Shiga Rudani Yayin Da Matasa Suka Farmaki Cocin RCCG, Sun Lalata Kayayyaki Da Dama

An Shiga Rudani Yayin Da Matasa Suka Farmaki Cocin RCCG, Sun Lalata Kayayyaki Da Dama

  • Wasu fusatattun matasa sun yi ɓarna a cocin RCCG ana cikin gudanar da Ibada
  • Matasan da suka ƙunshi maza da mata, sun lalata kayayyaki irinsu kujeru da gangunan cocin
  • Bidiyon ta'asar da suka yi ya yaɗu a shafukan sada zumunta inda jama'a suka tofa albarkacin bakunansu

Wasu matasa da ba a iya tantance ko su waye ba, sun farmaki cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG), inda suka hargitsa ta ana cikin gudanar da Ibada.

An ɗora bidiyon a shafin Curthbet Chinedu na TikTok, wanda ke nuna lokacin da matasan maza da mata ke tada hargitsi gami da lalata kayayyakin cocin.

Matasa sun kai farmaki a cocin RCCG ana cikin Ibada
Fusatattun matasa sun farmaki cocin RCCG ana tsaka da Ibada. Hoto: @curthbet.chinedu
Asali: TikTok

Yadda matasa suka farmaki cocin RCCG

Duk da dai ba a iya tantance ko a wane wuri ba ne lamarin ya faru, Legit.ng ta tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a ɗaya daga majami'o'in Fasto Enoch Adejare Adeboye.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da Malamin Addini a Najeriya Ya Cinnawa Wata Budurwa Wuta lokacin Addu'a

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cikin bidiyon za a iya ganin yadda matasan suka lalata kujeru da gangunan cocin, kafin daga bisani kuma suka tunkari faston da ke jagorantar Ibada a lokacin.

Faston ya yi iya bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya tsayar da su daga abinda suke aikatawa, sai dai dole ya haƙura daga ƙarshe ya sanyawa sarautar Allah ido.

Kalli bidiyon a nan ƙasa:

Martanin mutane kan hargitsin cocin RCCG

Masu amfani da kafar TikTok da dama sun tofa albarkacin bakunansu biyo bayan wallafar bidiyon hargitsin da aka samu a cocin RCCG kamar haka:

johnnyrich64 ya ce:

“Mai ɗaukar bidiyo !!! Na yafe ma ka saboda coci ka tsaya ka yi bidiyo. Amma idan a gaba ka ƙara ɗora bidiyo ba tare da bayani ba za ka ga abinda zan yi ma ka.”

Kara karanta wannan

Sojojin Juyin Mulkin Gabon Sun Zayyano Dalilai 4 Da Suka Sanyasu Kifar Da Gwamnatin Kasar

God's Favourite ya ce:

“Wannan abin baƙin ciki ne. Ya mutum zai yi haka a ɗakin Ubangiji.”

stanlo ya ce:

“Komai yana tafiya lafiya lau har zuwa lokacin da faston ya faɗi wata magana mara tsari.”

'Yan bindiga sun yi garkuwa da malaman coci 2 a Neja

Legit.ng a baya ta kawo mu ku wani rahoto kan garkuwa da wasu malaman coci biyu da 'yan bindiga suka yi a jihar Neja.

Lamarin ya faru ne a farko-farkon watan Agustan da muke ciki, inda masu garkuwa da mutanen suka je har gida suka yi awon gaba da malaman cocin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel