A Karon Farko Indiya Ta Yi Nasarar Saukar Da Kumbonta A Wani Yanki Na Duniyar Wata Bayan Rasha Ta Gaza

A Karon Farko Indiya Ta Yi Nasarar Saukar Da Kumbonta A Wani Yanki Na Duniyar Wata Bayan Rasha Ta Gaza

  • Kasar Indiya ta kafa tarihi bayan kumbon jannatin kasar ya sauka a kusurwar duniyar wata
  • An cilla kumbon Chandrayaan-3 a ranar Juma'a 14 ga watan Yuli inda ya samu sauka a yau Laraba 23 ga watan Agusta
  • Wannan na zuwa ne bayan kokarin cilla kumbon sau uku cikin shekaru 10 bayan kumbon Rasha ya tarwatse a hanya

Mumbai, Indiya - Kasar Indiya ta yi bajinta bayan kumbon jannatin kasar ya sauka a kusurwar duniyar wata a karon farko.

Kumbon ya sauka ne a yau Laraba 23 ga watan Agusta, kamar yadda Legit.ng ta tattaro.

Kasar Indiya ta kafa tarihi bayan kumbonta ya sauka a duniyar wata
Kasar Indiya Ta Yi Nasarar Saukar Da Kumbonta A Duniyar Wata. Hoto: ISRO/AFPTV and DIBYANGSHU SARKAR/AFP.
Asali: UGC

Yaushe Indiya ta cilla kumbon?

Rahotanni sun tabbatar da cewa kasar Indiya ta tura kumbon ne tun ranar Juma'a 14 ga watan Agusta 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Rashin Tausayi: Matar Aure A Bauchi Ta Kashe Jinjirin Kishiyarta

Wannan na zuwa bayan kumbon kasar Rasha ya tarwatse a kokarin isa kusurwar duniyar watan.

Kumbon Chandrayaan-3 na Indiya an cilla shi ne daga Kudancin kasar Indiya kamar yadda jaridar BBC ta ruwaito.

Fira ministan kasar Indiya, Narendra Modi shi ya tabbatar da saukar kumbon a kusurwar duniyar wata.

Karo na nawa Indiya ke tura kumbon?

Wannan shi ne karo na uku da kasar ke kokarin cilla kumbon nata zuwa duniyar wata tun a shekarar 2009 amma babu nasara sai yanzu.

Bayan shekaru 10, kasar ta sake kokarin cilla shi don kafa tarihi amma hakan ya ci tura sai a 2023.

Kumbon Chandrayaan-3 shi ne ya fara kafa wannan tarihi na isa kusurwar duniyar wata.

Yayin da ya ke tabbatar da hakan, Bayo Onanuga tsohon Daraktan kamfe na shugaban kasa ya ce:

"Indiya na kan gaba inda ta cilla kumbon ta na Chandrayaan-3 kusurwar kudu ta duniyar wata.

Kara karanta wannan

Barcelona Na Shirin Soke Karin Kumallon 'Yan Wasa Don Samun Rarar Kudade A Kungiyar, Ta Yi Karin Bayani

"Wannan wani bajinta ne bayan kumbon Rasha ya tarwatse a kokarin isa duniyar wata.
"Kasar da Nerandra Modi ke jagoranta ta zama na hudu a tarihi bayan Tarayyar Soviet da Amurka da kuma Sin sun yi nasara cilla kumbonsu zuwa duniyar wata."

Nan Kusa Najeriya Za Ta Tura Wakilinta Zuwa Duniyar Wata

A wani labarin, Ministan kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire a Najeriya, Ogbonnaya Onu ya jaddada muhimmancin ilimin kimiyya da fasaha da kere-kere ga ci gaban kasa.

Onu ya tabbatar da manufar gwamnatin Najeriya na tura wakilanta zuwa duniyar wata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel