Kungiyar Barcelona Za Ta Soke Tsarin Karin Kumallo Ga 'Yan Wasa Don Rage Kashe Kudade

Kungiyar Barcelona Za Ta Soke Tsarin Karin Kumallo Ga 'Yan Wasa Don Rage Kashe Kudade

  • Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta za ta kafa dokar hana 'yan wasa karin kumallo don rage kashe kudade
  • A bayyane ya ke Barcelona na shan daka tare da kame-kame wurin cinikin 'yan wasa cikin shekarun nan
  • Legit.ng Hausa ta ji ta bakin wasu masoya kwallon kafa da ke goyon bayan kungiyoyin kwallon kafa daban-daban

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Barcelona, Sifaniya - Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona za ta cire tsarin karin kumallo ga 'yan wasa don rage yawan kashe kudade.

Wani rahoto da Relevo ta fitar, ya tabbatar cewa kungiyar ta yanke shawarar cire karin kumallo ga matasan 'yan wasa.

Barcelona ta dauki matakin soke karin kumallo don rage kashe kudade
Kungiyar Barcelona Ta Dauki Matakin Ne Don Rage Yawan Kashe Kudade. Hoto: Twitter
Asali: Getty Images

Me Barcelona ta ce?

Rahoton ya kuma ce mafi yawan 'yan wasa ba sa samun karin kumallon, hakan ya ba wa shugaban kungiyar, Joan Laporta yanke shawarar cire tsarin karin kumallon da cewa ana kashe kudade babu adalci.

Kara karanta wannan

Meye zai faru? Shugaban matasan PDP ya bayyana kwarin gwiwar tsige Tinubu a mulki

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Transfer News Live ta wallafa a shafinta na Twitter cewa, Barca a kullum kokarin rage yawan kashe kudade ta ke, hakan ne ma ya sa ta daukar wannan mataki.

Ta ce ba ko wane dan wasa ba ne ke samun karin kumallon inda kungiyar ta ga hakan kawai kashe kudade ne ba tare da adalci ba.

Wane hali Barcelona ke ciki?

Ba a boye ya ke ba, Barcelona na shan daka idan aka kwatanta da sauran kungiyoyin kwallon kafa.

Wannan yanayi na matsin tattalin arziki da su ke ciki ya saka kungiyar daukar wasu matakai da ba a saba gani ba don rage kashe kudade a kungiyar.

A kakar wasa ta 2021, dole su ka bar shahararren dan wasansu, Lionel Messi barin kungiyar saboda sun gagara sabunta kwantiraginsa.

Kara karanta wannan

Wata miyar: Talauci ya sa Gambia ta hana shugaban kasa da jami'an gwamnati tafiya kasashen waje

Kungiyar ta yi kokarin dawo da Messi don ci gaba buga tambola amma hakan ya ci tura saboda gagara samun kudin da za su biya.

Martanin mutane kan tsarin na Barcelona

Legit.ng Hausa ta ji ta bakin wasu magoya bayan kungiyoyin kwallon kafa daban-daban.

Aminu Garba Umar ya ce shi ya na goyon bayan wannan mataki dari bisa dari inda ya ce wannan ba wata matsala ba ce.

Ya ce duk lokacin aka samu abin da ake so za a iya dawo da tsarin.

Ya ce:

"An yi haka ne don kungiyar ta tsaya da kafafunta, a baya da ba sa cikin matsala ai ba a yi haka ba.
"Duk lokacin da komai ya dawo dai-dai kungiyar ta farfado za ta iya mayar da wannan tsari."

A martanin Ibrahim Yahaya ya ce wannan tsari bai yi ba, idan za su nemi bashi kawai su nemo.

A cewarsa:

"Wannan wane irin tsari ne?, Idan za su nemi bashi kawai su ci, ai hakan ya na kashe kwarin gwiwar 'yan wasa.

Kara karanta wannan

Rikita-rikita Yayin Da Mata Ta Fashe Da Kuka Bayan Mai Tura Baro Ya Tsere Mata Da Kaya, An Ba Ta Taimako

"Babu wani dan kwallon gaske da zai je kungiyar saboda abun kullum baya ya ke kara yi."

Shamsuddeen Madrid ya ce wannan ai abin kunya ne, wane tasiri kudin karin kumallo zai yi wa kungiyar.

Ya ce:

"Gaskiya wannan abin kunya ne, babu abin da wannan zai kara musu, watakila a baya ma sun cire wasu abubuwa da ban sani ba."

Messi Ya Dara Ronaldo A Yawan Cin Kofuna

A wani labarin, Lionel Messi ya dara abokin hamayyarsa, Cristiano Ronaldo da yawan cin kofuna.

Messi a tarihi ya ci kofuna 41 yayin da Ronaldo ke da kofuna 40 kamar yadda kambun bajinta na Guinness ya fitar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel