Bola Tinubu Yana Kashe 'Yan Arewa da Sunan Yaki da Nijar Inji Naja’atu Muhammad

Bola Tinubu Yana Kashe 'Yan Arewa da Sunan Yaki da Nijar Inji Naja’atu Muhammad

  • Naja’atu Muhammad ba ta cikin wadanda hankalinsu ya kwanta da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu
  • Tun a lokacin kamfe, ‘yar siyasar ta ce ‘dan takaran na jam’iyyar APC bai da wata manufa domin Arewa
  • Ganin yadda aka tattago yaki da makwabta a Nijar, Naja’atu ta ce hakan ya nuna kiyayya ga Arewa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Tun can Naja’atu Muhammad ba ta yarda da kamun ludayin Bola Ahmed Tinubu, har gobe ta na ganin shugaban bai nufin Arewa da alheri.

A wata hira da aka yi da Hajiya Naja’atu Muhammad, ta soki gwamnatin Bola Tinubu kan yakin da ta ke shirin yi da Nijar, ta Arewacin Najeriya aka yaka.

‘Yar siyasar ta na da ja game da yadda APC ta lashe zaben 2023, ta na ganin an saba ka’idojin damukaradiyyar da ECOWAS ke so a dawwamar a Nijar.

Kara karanta wannan

"Ba Zan Yi Karya Domin Kare Gwamnatin Tinubu Ba" Sabon Minista Ya Yi Magana Mai Jan Hankali

Naja’atu Muhammad TINUBU
Naja'atu Muhammad ta soki Bola Tinubu Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Tinubu ya zama shugaban kungiyar ECOWAS ne saboda ya na mulkin Najeriya, Naja’atu take cewa ya kamata ya fara duba bukatun kasarsa kafin komai.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Hakkin da ya fara rataya a kan ka shi ne na ‘Yan Najeriya, ba ka tuntubi ‘yan Najeriya ba. Ba ka nemi izini daga ‘yan majalisa kamar yadda doka ta ce ba.
Haka kurum ka yi azarbabi ka ce za ka yaki Nijar, to Nijar da tayi mana mene? Ba ka da izinin shiga yaki da wata kasa idan ba kasar ce tayi mana barazana ba."

- Naja'atu Muhammad

Arewa da kasar Nijar

A hirar da aka yi da ita, ‘yar siyasar ta gargadi gwamnati cewa Nijar da Arewacin Najeriya tamkar kasa guda ce da 'yan mulkin mallaka su ka raba.

A Daular Usmaniyya, Hajiya Naja’atu Muhammad ta ce Nijar da bangaren na Najeriya su na dunkule ne, sai daga baya turawa su ka yagi rabonsu da yaki.

Kara karanta wannan

Juyin Mulki: Yayin Da ECOWAS, Nijar Su Ka Gaza Samun Daidaito, Fafaroma Francis Ya Shiga Tsakani

Baya ga dangantakar da Arewa ta ke da ita da Nijar, tsohuwar jagorar ta APC ta ce Jamhuriyyar tayi iyaka da jihohi bakwai wanda duk su ke Arewa.

Asarar dukiya a iyakokin Nijar

‘Yar gaba-gaban wajen tallata Atiku Abubakar ta ce a sakamakon rufe iyakokin Nijar da aka yi, ‘yan kasuwan kasashen nan sun yi asarar dukiya mai yawa.

"Wannan hauka da nade-nade, ni ina ganinsa a matsayin cin zarafin ‘Yan Arewa ba Nijar ba.
Yanzu a iyakokin da aka rufe, biliyoyin kudi sun salwanta. Wadanda su ka kawo tireloli na albasa ta narke, na san mai shigo da kifi na N200m, yanzu ya narke.“

- Naja’atu Muhammad

Kamaru da Sanagal su na cikin inda shugabannin farar hula ba su da niyyar barin ofis, saboda haka Naja’atu ta ke ganin a kyale Nijar ta zabi salon mulkinta.

Su kan su masu cewa za su yi yaki domin dawo da farar hula, su da kan su ba damukaradiyyar su ke yi ba.

Kara karanta wannan

100 sun mutu: Yanzu haka 'yan Boko Haram da ISWAP suna can suna ta kwabza yaki a Borno

Idan ka dauki Togo, shugabanta ya yi shekaru 38 a mulki. Sai da ya mutu, 'dan sa ya karba, yanzu ya yi shekaru 17.

Rashin tsaro a yankin Arewa

"Ka na da sojojin da fiye da shekaru 20 sun gaza yin maganin ta'addanci, sojojin ne za ka ce sun tafi wani yaki?
Ba Nijar ake yaka ba, Najeriya ake yaka. Tinubu bai taba boye kiyayyarsa da yake wa Arewa ba tun ya na gwamna."

- Naja’atu Muhammad

Taron jagororin ECOWAS a Aso Rock

Sojojin da su ka yi juyin mulki a Nijar sun ce sai zuwa 2026 za su sauka. Ana haka aka ji Shugaban Najeriya da jagororin kungiyar ECOWAS sun yi zama.

Abin da aka tattauna a zaman zai yi tasiri a kan matakin da za a dauka a kan Jamhuriyyar Nijar da aka kifar da shugabaMohammed Bazoum a Yuli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel