Fafaroma Francis Ya Bukaci Kasashen Duniya Su Shiga Tsakani Kan Rikicin Nijar Da ECOWAS

Fafaroma Francis Ya Bukaci Kasashen Duniya Su Shiga Tsakani Kan Rikicin Nijar Da ECOWAS

  • Sojojin mulkin Nijar sun bayyana cewa za su mika mulki ga farar hula amma bayan shekaru uku
  • Yayin da kungiyar ECOWAS ta yi fatali da wannan tsari inda ta ce ba za su lamunci wannan ganganci ba
  • Har ila yau, Fafaroma Francis yayin hudubarshi a cocin Vatican a ranar Lahadi ya roki sulhu da zaman lafiya a tsakani

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja – Tattaunawar da ake kokarin yi tsakanin tawagar kungiyar ECOWAS da shugaban sojin Nijar, Abdourahamane Tchiani ta ci tura.

Fafaroma Farancis ya yi martani kan wannan rikici a Nijar yayin hudubar ranar Lahadi 20 ga watan Agusta a Vatican, Legit.ng ta tattaro.

Fafaroma Francis ya bukaci kasashen duniya su shiga rikicin ECOWAS da Nijar
Fafaroma Francis Ya Yi Martani Kan Rikici Tsakanin Nijar da ECOWAS. Hoto: Bola Ahmed Tinubu/X, Tiziana Fabi/AFP and OTRN/Getty Images.
Asali: UGC

Meye Fafaroma ya ce game da Nijar da ECOWAS?

AP ta tattaro Fafaroma na kira ga zaman lafiya a Nijar inda ya bukaci dukkan bangarorin biyu da su nemo hanyar lalama.

Kara karanta wannan

ECOWAS Ta Bayyana Matsayinta Kan Shekaru Uku Da Shugaban Sojin Nijar Ya Ce Za Su Yi a Mulki

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da ya ke magana a dandalin St. Peter, Fafaroma ya ce:

“Ina addu’ar samun zaman lafiya da kira ga kasashen duniya su shiga tsakani don maslaha cikin gaggawa saboda samun daidaito ga kowa.”

A wata hira da 'yan jaridu a ranar Lahadi 2 ga watan Agusta, kwamishinan siyasa da zaman lafiya, Abdel-Fatau Musa ya ce Tchiani ya ki amincewa da tayin ECOWAS yayin da ya ce za su yi shekaru uku kafin mika mulki.

Kamar yadda Daily Trust ta tabbatar, Musa ya ce:

“ECOWAS ba ta bukatar wani tsarin ba da mulki mai tsayi a yankin, ya kamata su shirya mika mulki cikin kankanin lokaci.
“Mulkin soja ya yi yawa, idan su ka mika mulki cikin gaggawa ga gwamnatin farar hula don ci gaba da abin da ya dace, shi ne zai fi musu kyau.”

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Shugaban Nijar Ya Bude Baki, Ya Fadi Shekarun da Zai Yi kan Mulki

Meye martanin Tchiani a Nijar ga ECOWAS?

Rahotanni sun tattaro cewa Janar Tchiani yayin wata sanarwa a gidan talabijin a ranar Asabar 19 ga watan Agusta inda ya ce ba za su mika mulki ba sai bayan shekaru uku.

A cikin sanarwar har ila yau, Tchiani ya ce Jamhuriyar Nijar ba ta shirya shiga yaki ba kuma ba ta son shiga yaki amma za ta iya yi idan hakan ya zama dole.

Fafaroma Ya Yi Allah Wadai Da Kona Qur'ani A Sweden

A wani labarin, Fafaroma Francis ya yi Allah wadai da aika-aika da aka yi a kasar Sweden na kona Qur'ani mai girma.

Francis ya nuna barin ransa da kuma kyamatar wadanda su ka aikata haka inda ya ce dole a mutunta duk wani littafi mai tsarki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.