Ukraine ta dauki matakin da zai iya harzuka Putin yayin da ake kokarin kawo karshen yaki

Ukraine ta dauki matakin da zai iya harzuka Putin yayin da ake kokarin kawo karshen yaki

  • Mai girma shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya sa hannu domin su shiga kungiyar EU
  • Hadimin shugaban kasar, Sergii Nykyforov ya bada wannan sanarwa a shafinsa na Facebook a jiya
  • Volodymyr Zelensky ya dade yana neman Ukraine ta samu rajista da EU da kuma kungiyar NATO

Ukraine - A farkon makon nan ne aka ji Shugaba Volodymyr Zelensky ya sa hannu ya na rokon a sa kasar Ukraine a cikin ‘yan kungiyar EU ta tarayyar Turai.

Gidan yada labaran VOA ya kawo rahoto cewa Volodymyr Zelensky ya nemi alfarmar cewa kasar Ukraine ta shiga karkashin jeringiyar kungiyar kasashen EU.

Ana neman a bi wani irin tsari na musamman ne domin a biyawa Ukraine bukatarta. Hakan zai sa a kammala shirin ba tare da an dauki tsawon lokaci ba.

Kara karanta wannan

An shiga tsakani: Za a yi tattaunawar zaman lafiya tsakanin Ukraine da Rasha yau Litinin

Mai magana da yawun shugaban Ukraine, Sergii Nykyforov ya bada wannan sanarwa da yake magana a shafinsa a ranar Litinin, 28 ga watan Fubrairu 2022.

Sergii Nykyforov ya yi bayani a kan rattaba hannun da Volodymyr Zelensky ya yi a kan wadannan takardu, inda ya ce jiya rana ce ta tarihi a Ukraine.

Ukraine da Rasha
Volodymyr Zelensky da Vladimir putin Hoto: www.timesofisrael.com
Asali: UGC

Takardu za su kasar Belgium

An ga hotunan Zelenskyy a kafafen sada zumunta na zamani yayin da yake sa hannu a kan wadannan takardu. Babu mamakin hakan ya fusata Rasha.

Hadiman shugaban kasar sun tabbatar da cewa takardun su na kan hanyar zuwa Brussels. Amma Von der Leyen ya ce yi wa Ukraine rajistar zai dauki lokaci.

Yunkurin gwamnatin Zelensky

Kafin nan an ji Zelensky yana rokon kasashen Turai su amince da Ukraine a kungiyarsu, ya bukaci hakan ne bayan sojojin Rasha sun kawo masu hari.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Belarus ta shiga yakin Rasha, tana shirin danna dakarunta cikin Ukraine

Hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN ta ce tun a shekarar 2019 majalisar kasar Ukraine ta amince da kudirin da ya bada damar shigarsu EU da NATO.

A 2014 ne sabuwar gwamnatin da aka kafa a Kiev ta fara watsi da yarjejeniyar da aka yi a baya, ta soma kama hanyar cusa Ukraniyawa a kungiyoyin na Turai.

‘Yan majalisa sun yi wa dokoki garambawul domin shiga sahun EU ya yiwu cikin sauki. Tun daga wancan lokaci kasar ta dauki hanyar samun matsala da Rasha.

Tasirin yakin a Najeriya

A wani rahoto da muka fitar dazu, kun ji cewa yakin da Rasha ta ke yi a kasar Ukraine zai iya shafan tattalin arzikin kasar Najeriya, har ya jawo tsadar kaya.

A halin yanzu Najeriya ta kan yi sayayyen kayan biliyoyin kudi duk shekara daga kasar Rasha da makwabciyarta, yakin na su zai jawo asarar cinikin dalolin kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel